Gwamnatin Jihar Bauchi ta ce ba za ta lamunci kalaman tunzura jama’a daga duk wani mai wa’azi a jihar ba.
Sakataren gwamnatin jihar, Mista Ibrahim Kashim ne ya yi wannan gargadin yayin da yake zantawa da manema labarai sakamakon taron kwamitin tsaro na jihar, a ranar Litinin a Bauchi.
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin: Kasar Sin Ba Ita Ce Tushen Saka Wa Kasashen Afirka Tarkon Bashi Ba
- An Kama ‘Yansanda Biyar Da Dan Kasuwa A Filato
A cewarsa, gwamnati za ta tunkari duk wani mai wa’azi da ya yi kalaman da zai iya haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin jama’a.
“Kamar yadda kuka sani, muna fitowa ne daga cikin mawuyacin halin da ake ciki na yakin neman zabe kuma abubuwa da dama sun faru bayan zaben da ke bukatar tsauraran matakan tsaro.
“An yi ta hayaniya wasu kuma kan batutuwan da suka shafi wa’azi da fahimtar mahallin wa’azi da kuma abin da ya haifar.
“Mun damu saboda ba batun Akida ba ne, ba batun siyasa ba ne kawai batun tunzura maganganun da za su haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin al’ummarmu.
“Mun gana, mun tattauna kuma mun yanke shawarar cewa Bauchi wuri ne mai matukar zaman lafiya, kuma za mu yi duk abin da za mu iya don ganin an zauna lafiya.
“Ba za mu bari wani abu ko maganganun wani ya kawo cikas ga zaman lafiyar da muke samu a jihar ba,” in ji shi.
Kashim wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Tsaro, ya kara da cewa gwamnatin jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ya kara da cewa “Ba za mu kyale wani daga yanzu ya ci mutuncin wani ko cin mutuncin imanin wani ko wasu mutane dangane da imaninsu ba,” in ji shi.
Shi ma da yake jawabi, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Aminu Alhassan, ya bayyana cewa ana kokarin dakile ayyukan da za su iya kawo cikas ga zaman lafiya a jihar.