Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai ya bayyana cewa, a halin yanzu gwamnatinsa ta shirya tsaf don kafa rundunar tsaro ‘yan sa kai a jihar don tunkarar matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.
Gwamna ya bayyana haka ne ranar Alhamis a yayin da yake kaddamar da kashin na farko na jami’an kungiyar su 500.
- Gwamna Ortom Ya Bukaci A Saki Jagoran IPOB Nnamdi Kanu
- An Kashe Mutane Da Dama Da Kone Gidajensu A Wani Hari Da Aka Kai Benuwai
“Wannan lamari ne da ke bukatar jari mai matukar yawa, da mun so guje masa, amma ya zama tilas saboda yadda ‘yan ta’adda suka mamaye kasarmu dole mu dauki wannan matakin domin ceto al’umarmu.,” inj ji Ortom.
Gwamnan ya kuma kara bayyana cewa ayyukan ta’addanci ya tarwatsa mutane fiye da Miliyan 1.5 daga garuruwansu na haihuwa sun koma rayuwa a sansanin ‘yan gudun hijira.
Ya ce, gwamnati za ta nemo lasisin rike bindiga kirar AK47 da AK49 da sauran manyan makamai na zamani ga jami’an tsaronsu don su fuskanci ‘yan ta’addar a sasan jihar.
Cikin wadanda suku halarci taron kaddamarwa sun hada da Tor Tiv, Farfesa James Ayatse, inda ya yi alkawarin bayar da goyon baya don samun nasarar shirin.