Fitaccen Dan gwagwarmaya, mai fafutukar yaki da cin hanci da rashawa, Dakta Mahadi Shehu, ya bayyana cewa gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammad Buhari ita ce silar jefa al’ummar kasar nan halin da suke ciki na kuncin rayuwa da tabarbarewar tattalin arzikin Nijeriya.
Mahadi Shehu, ya bayyana haka ne a zantawarsa da manema labarai a Kaduna, inda ya bukaci gwamnatin Bola Tinubu da ta gayyaci tsohon shugaban kasa domin bayar da ba’asin yadda aka yi wasoso da dukiyar al’ummar kasar nan.
Ya ci gaba da cewa, “Buhari da makusantansa su ne suka kawo tsananin talauci, yunwa da fatara a kasar nan. Su ne kuma suka kawo karayar arziki ta mutane da suka hada da ‘yan kasuwa da manoma. Duk wani bala’i da muke ciki a yanzu, Buhari ne sila sanadiyyar rashin sanin makamar mulki.
“A karkashin mulkinsa an kashe dubban mutane tare da kone dukiyoyi wadda ba ta da iyaka,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp