Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo a ranar Litinin ya yi alkawarin biyan diyya ga iyalan mafarauta 16 da aka kashe.
Wasu gungun ‘yan banga ne suka kashe su a garin Uromi da ke Edo yayin da suke kan hanyarsu ta dawowa zuwa Kano.
- Atisayen Dakarun PLA Horo Ne Mai Tsanani Ga Masu Rajin Neman ’Yancin Kan Taiwan
- Sanusi II Ya Gudanar Da Hawan Nassarawa Duk Da Umarnin ‘Yansanda A Kano
Ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da ya samu rakiyar takwaransa na jihar Kano, Abba Yusuf, inda ya kai ziyarar jaje ga iyalan mafarautan a Torankawa da ke jihar Kano.
“Muna shirye-shiryen bayar da diyya ga duk wadanda lamarin ya shafa.
“Ina kuma yabawa mutanen jihar Kano da daukacin arewa saboda rashin daukar doka a hannunsu da kai harin ramuwar gayya,” inji shi.
Ya yi addu’ar Allah ya jikan mafarautan da suka mutu.
Gwamnan Edo ya kara, da cewa, tuni aka fara cafke wadande ake zargi da aikata wannan aika-aika.
“An riga an kama kimanin mutane 14 da ake zargi, za mu ci gaba da bin diddigin lamarin har sai an gurfanar da su a gaban kotu an yi wadanda aka kashe adalci”. In ji Okpebolo
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp