Gwamnatin Jihar Gombe ta umarci Ma’aikatar Lafiya ta jihar da hukumar yaƙi da cutar sida ta jihar (GOMSACA) da kuma hukumar kula da lafiya a matakin farko ta Jihar da su samar da dabarun ɗorewar nasarorin da aka samu a yaƙi da cutar ta Sida a jihar.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njoɗi, ne ya bayar da wannan umarnin yayin da ya karɓi baƙuncin babbar tawagar yaƙi da cutar Sida ta Jihar Gombe (GOMSACA) bisa rakiyar Hukumar Yaki da Cutar Sida ta ƙasa (NACA), da Cibiyar Kula da Shirye-shiryen Kiwon Lafiya (CIHP) tare da sauran masu ruwa da tsaki da kuma abokan hulɗa a wata ziyarar da suka kai a gidan gwamnati.
- Sallah: Yadda Sarkin Gombe Ya Jagoranci Hawan Daba
- Hutun Haihuwa: An Samu Masu Yin Tazara 28,561 A Farkon 2023 A Jihar Gombe
Sakataren ya ce; cutar Sida wata abar damuwa ce ga gwamnatin jihar, yana mai bada tabbacin cewa za ta yi duk mai yiwuwa don daƙile yaduwarta a jihar.
Da yake yabawa tawagar bisa jajircewarta na rage illar cutar a jihar, Farfesa Njoɗi, ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar zata tabbatar da ɗorewar yaƙin da tabbatar da nasarorin da aka samu ta hanyar jajircewa da gudummawar da abokanan hulɗar ci gaba suka bayar.
“Mun fahimci damuwar ku game da ɗorewar wannan shiri, ba za mu ci gaba da zama mabarata ba; muna jiran tallafi daga abokan hulɗar ci gaba a ko da yaushe, kowa yana ƙoƙari ya bayar da ta shi gudummawa a duniya, dole ne muma mu yi iya bakin ƙoƙarinmu wajen yiwa jama’a hidima”.
Don haka sakataren ya umurci ma’aikatar lafiya da hukumomin da abin ya shafa da su samar da hanyoyin da za a ci gaba da yaki da cutar da ɗabbaƙa nasarorin da aka samu.