Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya karbi bakuncin mai martaba Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar da sauran masu sarautar gargajiya a ziyarar bikin babbar sallah.
Hawan dabar na cikin al’adun gargajiya da ake yi duk shekara a gidan gwamnati wanda sarki ke jagorantar hakimai da ‘yan majalisar sarkin.
- Gwamnatin Kano Za Ta Bincike Dakatar Da Albashin Ma’aikatan KanoÂ
- Ban Yi Nadamar Rusau A Kano Ba -Gwamnan Kano
A jawabin da ya gabatar a wajen bikin, Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar, ya yaba tare da jinjina wa gwamnatin jihar bisa kokinta a bangaren kyautata shugabanci da kula da rayuwar al’umma.
Sarkin, wanda shi ne shugaban majalisar sarakunan jihar, ya tabbatar wa Gwamna Inuwa goyon bayan masarautun gargajiya a jihar domin amfanin al’umma baki daya.
Daga bisani sarkin ya jagoranci daruruwan mahaya dawaki a hawan dabar.
A nasa bangaren, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa nasarorin da gwamnatinsa ta samu na da alaka da goyon baya da kyawawan shawarwarin sarakuna da malaman Addini da shugabannin siyasa.
“Nasarorin nan ba ni kadai na same su ba, har da shugabannin siyasa da na gargajiya da na Addini da matasa maza da mata wadanda suka taka rawar gani wajen ganin mun samu wadannan nasarori, don haka muna godiya ga kowa da kowa.”
Kazalika ya bayyana cewa duk da dimbin kalubalen zamantakewa da tattalin arziki da ake fuskanta, gwamnatinsa ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen samar da muhimman ababen more rayuwa ba.
Gwamnan ya yi kira ga sarkin Gombe da sauran sarakunan jihar da kada su yi kasa a gwiwa wajen neman dama da hanyoyin da za su kara kawo ci gaba a jihar.
Ya kuma tabbatarwa jama’ar jihar cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen neman goyon baya daga sarakunan gargajiya domin gudanar da mulkin jihar cikin adalci.
Ya kuma yi godiya ga Allah Madaukakin Sarki da Sarkin Gombe da ya jagoranci ‘yan majalisarsa da sauran al’ummar musulmi zuwa ziyarar a gidan gwamnati domin gudanar da gaisuwar Sallah.
Kazalika Gwamna Inuwa ya mika godiyarsa bisa karramawar da suka yi masa tare da jaddada kokarin gwamnatinsa ga Jihar Gombe.