Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya ba da umarni karkashin doka mai lamba 002 ta 2023 na kafa hukumar samar da ruwan sha da tsaftar muhalli a kananan garuruwan Jihar Gombe (STWSSA).
Ya ce, hakan wani mataki ne na samar da tsaftataccen ruwan sha da lafiyayyen muhalli a fadin Jihar Gombe bisa ka’idoji da tanade-tanaden kasa da kasa don samun ci gaba.
- Kasashe 5 Da Nijeriya Ta Fi Shigo Da Kayayyakinsu
- NFF Ta Kaddamar Da Sabon Filin Wasan Kwallon Kafa A Birnin Kebbi
Dokar ta zayyano cikakken tsarin kawo sauyi na samar da ruwa da tsaftar muhalli a birane da kauyuka na Jihar Gombe.
Da yake tsokaci kan bukatar samar da ingantaccen ruwan shan, Gwamna Inuwa ya jaddada kudurin jihar na inganta rayuwa da bunkasa ci gaban tattalin arziki mai dorewa a karkashin wannan shiri.
Karkashin sabuwar hukumar samar da ruwan da aka kafa (STWSSA), aikace-aikacenta sun shafi bangarori da dama. An dora mata alhakin sanya ido kan muhimman sassan da suka shafi ruwa da tsaftar muhalli a dukkan kananan garuruwan da ke fadin jihar.