Gwamnatin Jihar Gombe ta cimma matsayar fadada wasu muhimman hanyoyi biyu na Ture zuwa Dogon Ruwa zuwa Gelengu, dana Bakasi zuwa Gelengu, wadanda gwamnatin baya ta fara.
Kwamishinan Ayyuka da Sufuri na jihar Injiniya Abubakar Musa Bappa ne ya bayyana hakan ranar Larabar yayin wani taron manema labarai kan sakamakon zaman majalisar zartarwa ta jiha karo na 23 daa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya jagoranta a zauren majalisar zartaswa ta jiha dake gidan gwamnati.
Ya ce, “Hanyar Ture zuwa Dogon Ruwa mai tsawon kilomita 23, gwamnatin da ta gabata ce ta bayar da aikin ta a 2013 kan kudi Naira biliyan 2 da miliyan 600 amma ta yi watsi da ita saboda rashin biyan ‘yan kwangila, amma gwamnatin Muhammadu Inuwa Yahaya ta ga dacewar karisa aikin tare da tsawaita hanyar da kimanin kilomita 19 zuwa Gelengu dake karamar hukumar Balanga bisa karin kudi Naira biliyan 2 da miliyan 900”.
Kwamishinan ya ce shi ma aikin hanyar Bakasi zuwa Talasse da aka yi watsi da ita mai tsawon kusan kilomita 10 wacce ta hade kauyuka da dama za a kammala ta kan kudi Naira biliyan 2 da miliyan 600. Ya ce “Idan aka kammala aikin, hanyar zata bunkasa harkokin noma da tattalin arziki da zamantakewar al’ummomin wannan yankin”.
Ya kara da cewa majalisar ta kuma amince da daga darajar aikin titin Dukku zuwa Jamari mai tsawon kimanin kilomita 6 a karamar jukumar Dukku kan kudi Naira miliyan 557.
Injiniya Bappa ya ce ma’aikatar ta ziyarci wasu hanyoyi da dama da suka zagwanye sakamakon ruwan sama, inda wasu su ma suka yanke, yana mai cewa “Gwamnatin jihar ta tantance yanayin lalacewar hanyoyin kuma ta fara daukan matakan gyara”.
A nasa bangaren, Kwamishinan Kudi da Bunkasa Tattalin Arziki na Jihar Muhammad Gambo Magaji, ya ce majalisar ta amince da tsarin kashe kudaden na matsakaicin zango daga 2023 zuwa 2025 don mikawa Majalisar Dokokin Jiha tayi dubi tare da amincewa da shi.