Majalisar zartaswar jihar Jigawa ta amince da fitar da naira biliyan 2.5 don nazarin yanayin kasa domin gano yuwuwar samun makamashin Uranium, ɗanyen mai da iskar gas a cikin jihar.
Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na Jihar, Hon. Sagir Musa ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan taron majalisar zartarwar jihar a ranar Laraba.
- Adadin Yawon Shakatawa Da Mutanen Sin Suka Yi A Cikin Gida Ya Zarce Biliyan 4.998 Tsakanin Janairu Da Satumban Bana
- Nesa Ta Zo Kusa: Maraba Da Sabon Jirgin Kasa Samfurin CR450 Da Kasar Sin Ta Kera
Ya bayyana cewa, amincewa da binciken a wasu keɓantattun wurare, ya biyo bayan karatun share fage na shekaru da rahotanni kan albarkatun ma’adanai daban-daban a fadin jihar Jigawa.
Hon. Musa ya kara da cewa, aikin zai mayar da hankali ne kan nazari da binciken kimiyyar kasa a yankunan da ake tunanin cewa suna dauke da uranium, danyen man fetur, da iskar gas, da nufin tattara dukkan bayanan da ake bukata don ci gaba da aiki.
A cewar kwamishinan, amincewar wani bangare ne na manufofin gwamnatin Gwamna Umar Namadi na binciko albarkatun ma’adanai na jihar don haɓaka tattalin arzikin cikin gida mai ɗorewa.