Gwamnatin jihar Kaduna ta bada tabbacin kudirinta na inganta daidaiton jinsi da kuma tafiya da Mata a dukkan shirye-shiryenta na kawo cigaba.
Mataimakiyar gwamnan jihar, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe ce ta bayyana haka a wani taro da aka shirya kan nauyin da ya rataya akan jjinsi mabanbanta, wanda kungiyar Mata ta Majalisar Dinkin Duniya tare da hadin guiwar Bankin Raya Afirka (AfDB) da Gidauniyar Zamani suka shirya a Kaduna.
Dakta Balarabe ta bayyana cewa, gwamnatin Sanata Uba Sani ta yi imanin cewa, baiwa Mata dama ba wai kawai ya dace ba ne, babbar dabara ce ta habbaka tattalin arzikin jihar wanda za su iya bunkasa ci gaba, rage talauci, da inganta hadin kan al’umma.
A cewar Dokta Hadiza Balarabe, Nijeriya ta zama cikakkiyar kasa, dole ne ta tafi da Mata don su ne rabin al’ummar kasar kuma a daina tauye su ta hanyar cin zarafinsu.
Ta nanata cewce, Mata suna fuskantar tauyewa a zamantakewa da ra’ayoyin al’adu da ke lalata karfin tattalin arzikinsu da jagoranci, kamar wariyar jinsi, tsangwama, da kuma son zuciya.
Mataimakiyar Gwamnan, ta kara da cewa, al’amuran da suka shafi mata a koyaushe abin farin ciki ne a zuciyarta inda ta ce, “a matsayina na Mace kuma Uwa, kullum ina fuskantar wadannan kalubale. Mata ba su da cikakkiyar damar samun jarin kasuwanci, fasaha, kwarewa, da bayanai kamar yadda Maza ke samu”.
A nata jawabin, wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya kan harkokin Mata a Nijeriya da kungiyar ECOWAS, Beatrice Eyong, ta ce kashi daya ne kacal na harkar saye da sayarwa a Nijeriya ke zuwa ga bangaren Mata ‘yan kasuwa, don haka akwai bukatar shirya taro don horaswa ta yadda za a lalubo mafita.
A nata jawabin, Shugabar Gidauniyar Zamani, Misis Talatu P. Zamani-Henry ta bayyana cewa, an shirya taron ne domin shawo kan kalubalen daidaiton jinsi kan samar da damar shigo da kayayyaki a jihar Kaduna da kewayenta.