Gwamnatin Jihar Katsina ta sake jaddada kudurinta na tallafa wa ‘yansanda wajen tabbatar da doka da oda a lokacin da bayan gudanar da manyan zabuka masu zuwa a jihar.
Gwamna Aminu Bello Masari shi ya ba da wannan tabbacin a lokacin da amsar bakuncin sabon mataimakin babban sufeton ‘yansanda mai kula da shiyya 14 da aka tura, wanda suka kunshi jihohin Katsina da Kaduna da ya suka ziyarce shi.
Masari ya jaddada cewa gwamnatin jiha za ta yi duk abin da ya kamata domin kare al’ummarta daga duk wata barazana. Sai dai ya ce Jihar Katsina na bukatar karin jami’an ‘yansanda domin samar da tsaro yadda ya kamata. Daga nan sai ya yi wa mataimakin babban sufeton ‘yansanda fatan samun nasara wajen gudanar da sabon aikinsa.
Tun da farko, mataimakin babban sufeton ‘yansanda, Ahmed Abdurahman ya ce ya je gidan gwamnati ne musamman domin sanar da gwamnan jihar cewa an turo shi ne domin sa ido wajen gudanar da babban zaben 2023.
Abdurahman wanda aka turo daga kwalejin horas da ‘yansanda da ke Wudil a Jihar Kano, ya ce kwamishinan ‘yansanda na jiha ya yi masa bayani a kan shirye-shirye tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Ya ce haka kuma zai keyawa shiyoyin domin tabbatar da cewa an tanaji duk abin da ake bukata.
Kwamishinan ‘yansanda, CP Kolo Yusuf wanda tuni ya kama aiki da kuma fara shirye-shiryen daukar matakai na samar da tsaro.
Bayanin haka na kunshe a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Gambo Isa ya fitar.
Sanarwa tagargadi masu karya doka da suka hada da ‘yan bindiga, ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka ko dai su bar jihar ko kuma a damke su tare da hukunta su daidai yadda doka ta tanada.
A kan haka ne, rundunar ke kira ga al’ummar jihar su ci gaba da bayar da goyon baya da hadin kai ga ‘yansanda don tabbatar da samun cikakkiyar nasarar gudanar da zabukan shekarar 2023 cikin kwanciyar hankali da lumana.