An gargadi waɗanda aka naɗa muƙaman siyasa a Jihar Kaduna da su kiyayi yin rubuce-rubuce marasa kyau da rashin hankali a shafukan sada zumunta, domin irin waɗannan ayyuka na iya haifar da ɓata suna da martabar gwamnati.
Wannan gargadi ya fito ne daga sanarwar da aka fitar bayan taron horo na kwanaki biyu da aka shirya ta hannun Ofishin Shugaban Ma’aikata da Sakataren Gwamna Uba Sani, wanda ya gudana daga 4 zuwa 5 ga Disamba.
- NEMA Ta Raba Kayan Tallafi Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Kaduna
- Kaduna: Gwamnatin Tarayya Ta Fara Sayar Wa ‘Yan Jarida Buhun Shinkafa A Kan Naira 40,000
Sanarwar, wadda Alhaji Waziri Garba, mstaimakin shugaban harkokin gudanarwa, da Malam Ibraheem Musa, Kakakin Gwamnan, suka sa hannu, ta nuna cewa aiyukan gwamnatin Jihar Kaduna suna ƙarƙashin kulawar takamaiman ƙa’idoji na gudanar da aiki, ciki har da
“Tsarin Ayyuka, Tsare-Tsare Dokokin Kayan Aiki, Jagorar na Gudanarwa, da Dokokin Kuɗi.”
Haka nan, ko adawar siyasa an shawarci su daina yin rubuce-rubuce marasa ma’ana a shafukan sada zumunta, saboda irin waɗannan maganganu na iya zama kuskure da ake ɗauka a matsayin ra’ayin gwamnati, wanda zai iya haifar da mummunar martani ko hargitsi a cikin al’umma.