Hukumar tabbatar da ingancin makarantu ta jihar Kaduna (KSSQAA), ta gargadi masu makarantu masu zaman kansu kan kara kudin makaranta ba tare da samun amincewar gwamnatin jihar a hukumance ba.
A wata takarda mai kwanan ranar 7 ga Satumba, 2023, wacce Mercy Bainta Kude, Daraktar Sashen Makarantu masu zaman kansu ta sanya wa hannu a madadin Darakta-Janar, Hukumar ta jaddada cewa “babu wani ko wata mai makaranta da zai ko za ta kara kudin makaranta ko inganta makarantar ba tare da amincewar KSSQAA ba.”
- Yadda Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Yaya Da Ƙannuwa Da Wasu A Zaria
- Majalisa Ta Bai Wa Minista Sa’o’i 48 Ya Bayyana A Gabanta Kan Hatsarin Jirgin Abuja Zuwa Kaduna
Umurnin ya zo ne a daidai lokacin da gwamnati ke kokarin rage kudaden makaranta a makarantun mallakar jihar tare da tabbatar da bin ka’idojin da suka dace a fannin ilimi.
A cewar sanarwar, masu gudanar da makarantu masu zaman kansu dole ne su cika wasu sharuɗɗa kafin su nemi ƙarin kuɗin makaranta.
Waɗannan sharuɗɗa sun haɗa da shaidar cewa, daga ƙarin farko zuwa na biyu,dole sai an ɗauki aƙalla shekaru uku, ƙungiyar iyayen yara da Malamai ta amince da ƙudurin buƙatar ƙarin kuɗin makarantar a yayin taronta sannan babban daraktan makarantar ya rubuto takarda a hukumance ta neman ƙarin kuɗin makarantar.
Kude ta ƙara gargaɗin masu makarantu da su bi waɗannan sharuɗɗa, inda tace, bin dokar ya zama dole don tabbatar da gaskiya da rikon amana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp