Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya amince da fitar da kudin fansho Naira Biliyan 3.1 ga ma’aikatan da suka yi ritaya da kuma iyalan wadanda suka rasu a matsayin tallafi kan halin rayuwar da ake ciki.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Muhammad Lawal Shehu ya fitar a ranar Alhamis.
- Tabbatar Da Daidaito Da Cin Moriyar Juna Suna Cikin Babban Ruhin Shawarar BRI
- Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace
Ranar Abinci Ta Duniya: Gwamnatin Kaduna Za Ta Samar Da Tsaftataccen Ruwa Da Abinci Mai Gina Jiki
Mutum 38 Sun Mutu, 40 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Yobe
Sanarwar ta ce, matakin ya yi daidai da kudurin Gwamna Sani na rage wahalhalun da tsofaffi masu rauni ke fuskanta a jihar.
Sanarwar ta kuma ce, “Gwamna Sani ya jajirce wajen ganin cewa, ma’aikatan da suka yi wa jihar Kaduna aiki tukuru suna samun cikakkiyar damar samun abin da ya dace bayan sun bar aiki.
“Gwamnatin jihar Kaduna, ta hannun hukumar fansho ta jihar, ta jajirce wajen ganin an ci gaba da fitar da wadannan kudade ga wadanda yi wa jihar aiki tukuru.
Sanarwar ta ce “Hukumar Fansho ta Jiha za ta fitar da cikakken jerin sunayen da cikakkun bayanan wadanda za su amfana da kudaden a cikin ‘yan kwanaki massanarwar.0ffin ji sanarwar.