Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani ya ce, gwamnati ta kammala shirye-shirye da hadin guiwar jami’an tsaro musamman ‘Operation Safe Haven’ na mayar da al’ummomin Kudancin Kaduna da suka yi gudun hijira sabida ta’addancin ‘yan bindiga zuwa gidajensu.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron majalisar tsaron jihar da aka gudanar a gidan gwamnatin Sir Kashim Ibrahim, a ranar Laraba a Kaduna.
- Za Mu Bayyana Duk Wata Kwangila Da Gwamnati Ke Aiwatarwa – Minista
- Za Mu Karfafa Yaki Da Miyagun Kwayoyi A Jihar Zamfara – Gwamna Lawal
Gwamnan ya shaidawa shugaban hafsoshin sojan Nijeriya ta shiyya ta uku da kuma shiyya ta daya, Manjo Janar AbdulSalam Abubakar da Manjo Janar Valentine Okoro cewa, gwamnatinsa a shirye take ta samar da duk wani kayan aiki da suka dace don sake tsugunar da al’ummomin da suka rasa matsugunansu sakamakon ayyukan ta’addanci a yankin zuwa gidajen iyaye da kakanni.
A cewarsa, gwamnati za ta taimaka wa mutanen da suka rasa matsugunansu domin sake gina yankunansu da aka lalata idan bukatar hakan ta taso.
Tun da farko a nasa jawabin, shugaban hafsoshin sojan Nijeriya ta shiyya ta uku (GOC 3 Division) kuma kwamandan Operation Safe Haven, Manjo Janar AbdulSalam Abubakar ya ce, kashi na farko na sake tsugunar da jama’ar, za a fara ne da kauyuka 15.