Gwamnatin Jihar Kaduna ta sha alwashin gudanar da bincike kan musabbabin ruftawar masallacin fada mai dimbin tarihi da ke Zariya.
Masallacin ya rufta ne a yammacin ranar Jumu’a 11 ga watan Agustan 2023 yayin da ake shirye-shiryen fara Sallar La’asar.
Gwamnan Jihar Kaduna, Mai Girma Sanata Uba Sani ya karbi labarin rugujewar babban masallacin Zariya cikin kaduwa inda ya nuna alhininsa ga wadanda suka rasu da kuma wadanda suka jikkata.
Gwamnan ya jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa tare da addu’ar Allah ya jikan wadanda suka jikkata ya kuma basu lafiya.
Gwamnan ya godewa Mai Martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli bisa irin rawar da ya taka wajen hada kan al’ummarsa wajen gudanar da ayyukan ceto da bayar da agajin gaggawa ga wadanda suka jikkata.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa, tuni tawagar wasu manyan jami’an gwamnati karkashin jagorancin sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Balarabe Abbas Lawal suka isa Zariya domin duba halin da ake ciki da kuma halartar jana’izar wadanda suka rasu.
Babban Masallacin fadar da ya rufta, an gina shi tun a shekarun 1830.