Majalisar zartaswar jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Yusuf, ta amince da biyan bashin albashin watanni tara ga ma’aikatan tsaftar muhalli 2,369 a fadin jihar.
An amince da biyan bashin kudaden ne na watanni tara daga watan Yuni, 2024 zuwa Fabrairu, 2025.
- An Nuna Nezha 2 A Zama Na Musamman A Hedikwatar MDD Dake Birnin New York
- ‘Yansanda Sun Kama Wasu Mutane 2 Da Ake Zargi Da Yi Wa Yarinya ‘Yar Shekara 12 Fyade A Yobe
Kwamishinan ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi, Dahir M. Hashim ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano ranar Talata.
A cewarsa, amincewar wani gagarumin yunkuri ne na tallafawa dorewar tsafar muhalli a jihar.
Ya yaba da yadda jihar ke ci gaba da kokarin inganta rayuwar ‘yan jiharta da kuma tsaftar muhalli.