• English
  • Business News
Tuesday, September 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Kano Ta Fara Biyan Tsoffin Kansiloli Na APC Sama Da Naira Biliyan 16

by Abubakar Sulaiman
4 months ago
in Labarai
0
Gwamnatin Kano Ta Fara Biyan Tsoffin Kansiloli Na APC Sama Da Naira Biliyan 16
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da biyan sama da naira biliyan 16 na hakkokin ritaya da wasu alawus ga tsoffin kansiloli da sauran masu rike da mukaman siyasa a kananan hukumomi 44 na jihar. Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya jagoranci bikin kaddamarwar a ranar Laraba, inda ya bayyana cewa wannan biyan hakkoki ba alfarma ba ce, sai dai hakkinsu ne bisa adalci da godiya ga ayyukan da suka yi.

Gwamna Yusuf ya bayyana cewa wadanda suka ci gajiyar wannan tsari sun hada da kansiloli, mataimakan shugabannin karamar hukuma, shugabannin karamar hukuma, kwamishinonin gudanarwa da kuma mashawarta na musamman da suka yi aiki daga shekarar 2014 zuwa 2024. Ya ce gwamnatin NNPP ba za ta ci gaba da irin rashin adalcin da gwamnatin baya ta yi musu ba, inda ta ki biyansu hakkokinsu na ritaya.

  • ‘Yansanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Kisan Wata Matar Aure, ‘Yar shekara 22 A Kano
  • Gwamnatin Kano Ta Yi Barazanar Hukunta Matasa Masu Janyo Rikice-Rikice

An raba biyan kudi zuwa matakai uku:

  • Sashi na A (2014–2017): Naira biliyan 1.8 ga mutane 903 (za a biya nan take)
  • Sashi na B (2018–2020): Naira biliyan 5.6 ga mutane 1,198 (za a biya daga Mayu zuwa Yuli 2025)
  • Sashi na C (2021–2024): Naira biliyan 8.2 ga mutane 1,371 (za a biya daga Agusta zuwa Nuwamba 2025)

Haka kuma, an ware naira biliyan 1.27 don biyan kudin gidaje da kayan daki ga masu rike da mukaman siyasa na yanzu a kananan hukumomi.

Gwamna Yusuf ya kara da cewa wannan mataki alamar girmamawa ne ga masu yi wa kasa hidima, tabbatar da alkawari da kuma nuna amana a shugabanci. Ya yaba da kokarin dukkan bangarorin da suka taimaka wajen tabbatar da sahihancin wadanda suka cancanci biyan da kuma aiwatar da tsarin yadda ya kamata. Ya kuma roki hadin kai da goyon bayan al’umma wajen gina Jihar Kano mai cike da adalci da ci gaba.

Labarai Masu Nasaba

An Yi Garkuwa Da Wani Mai Hidimar Ƙasa Da Ɗalibi A Jos

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Hutun Sati 2 A Ƙasar Faransa

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: APCkano
ShareTweetSendShare
Previous Post

Sin Na Maraba Da Kamfanonin Kasa Da Kasa Har Da Na Amurka 

Next Post

Buhari Ya Yabi Tinubu, Ya Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Rage Tsammani Da Dogon Buri

Related

Sauye-sauyen Manufofin Gwamnati Na Iya Hana Masu HND Zuwa NYSC
Labarai

An Yi Garkuwa Da Wani Mai Hidimar Ƙasa Da Ɗalibi A Jos

1 hour ago
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Hutun Sati 2 A Ƙasar Faransa
Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Hutun Sati 2 A Ƙasar Faransa

2 hours ago
Sojoji
Labarai

Sojoji Sun Harbe Wasu ‘Yan Ta’adda 2 A Taraba

3 hours ago
Buhari Ya Taya Amusan Murnar Lashe Zinari A Gasar Tsere Ta Duniya
Labarai

Tinubu Ya Taya Amusan Da Gumel Murnar Samun Nasarori A Ɓangarori Daban-daban

4 hours ago
NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano
Manyan Labarai

NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano

6 hours ago
Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Ta Haifar Da Damar Wanzar Da Daidaito Da Adalci
Ra'ayi Riga

Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Ta Haifar Da Damar Wanzar Da Daidaito Da Adalci

7 hours ago
Next Post
Buhari Ya Yabi Tinubu, Ya Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Rage Tsammani Da Dogon Buri

Buhari Ya Yabi Tinubu, Ya Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Rage Tsammani Da Dogon Buri

LABARAI MASU NASABA

Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani

Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani

September 16, 2025
Sauye-sauyen Manufofin Gwamnati Na Iya Hana Masu HND Zuwa NYSC

An Yi Garkuwa Da Wani Mai Hidimar Ƙasa Da Ɗalibi A Jos

September 16, 2025
Sin Da Amurka Sun Yi Tattaunawar Keke-da-keke Kan Batutuwan Cinikayya Da Manhajar TikTok

Sin Da Amurka Sun Yi Tattaunawar Keke-da-keke Kan Batutuwan Cinikayya Da Manhajar TikTok

September 16, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Hutun Sati 2 A Ƙasar Faransa

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Hutun Sati 2 A Ƙasar Faransa

September 16, 2025
Sin Da Ghana Na Fadada Hadin Gwiwa A Bangaren Ciniki Da Zuba Jari

Sin Da Ghana Na Fadada Hadin Gwiwa A Bangaren Ciniki Da Zuba Jari

September 16, 2025
Sojoji

Sojoji Sun Harbe Wasu ‘Yan Ta’adda 2 A Taraba

September 16, 2025
Yawan Hatsin Da Aka Girbe A Kasar Sin Tsakanin Shekarar 2021-2025 Ya Kai Wani Sabon Matsayi

Yawan Hatsin Da Aka Girbe A Kasar Sin Tsakanin Shekarar 2021-2025 Ya Kai Wani Sabon Matsayi

September 16, 2025
Buhari Ya Taya Amusan Murnar Lashe Zinari A Gasar Tsere Ta Duniya

Tinubu Ya Taya Amusan Da Gumel Murnar Samun Nasarori A Ɓangarori Daban-daban

September 16, 2025
Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire

Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire

September 16, 2025
NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano

NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano

September 16, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.