Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da dashen bishiyoyi miliyan uku a fadin kananan hukumomin jihar 44 tare da hadin gwiwar kungiyar Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (ACReSAL).
A yayin bikin kaddamar da shirin a ranar Lahadin da ta gabata, gwamnan ya dasa bishiya a kan titin ‘state road’ da ke kan hanyar zuwa gidan gwamnatin jihar.
- APC A Kano Ta Kori Shugabannin Jam’iyyar A Matakin Unguwa Da Suka Dakatar Da Ganduje
- Babu Inda Mayaudara Da Mahassada Suka Taru Kamar Masana’antar Kannywood – Adam Zango
Gwamnan ya ce, za a dasa bishiyoyi a kan manyan titunan kananan hukumomin jihar, inda ya bukaci mazauna jihar da su fara dashen bishiyoyi a gidajensu da tituna da sauran wurare.
“Za a raba irin shuka miliyan uku a dukkan kananan hukumomin jihar 44. Za a dasa kusan iri miliyan 1.2 a manyan tituna a cikin manyan biranen jihar.” in ji gwamnan.
Shima da yake nasa jawabin, kodinetan ayyukan kungiyar, Dr. Dahir Muhammad Hashim ya ce, an kaddamar da aikin ne domin magance matsalar sauyin yanayi, wanda ya jefa jihar cikin matsanancin zafi a kwanakin baya.