Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da kwamitin kar-ta-kwana domin magance matsalar haramtattun gine-gine da ake yi ba tare da sahalewar hukumar tsara birane ta Jihar Kano ba.
Shugaban hukumar tsara birane na Jihar Kano, Arch. Ibrahim Yakubu Adam ne ya bayyana haka a lokacin kaddamar da kwamitin a Kano.
- Akwai Hannun Gwamnan Kano Wajen Fitar Da Murja Kunya Daga Gidan Gyaran Hali – Jaafar Jaafar
- Matakin Kona Kai Da Sojin Amurka Ya Dauka Ya Diga Ayar Tambaya Ga ‘Yan Siyasar Amurka
Ya bayyana dalilam kaddamar da kwamitin wanda hakan na cikin kyawawan tsare-tsaren gwamnatin Kano domin mayar da jihar daya daga cikin jihohin kasar nan da suka fi kyan fasali.
Shugaban hukumar ya nuna matukar damuwarsa bisa yawaitar filaye da ba su da rajista ko sahalewar hukumar, Inda ya gargadi masu shirya wannan mummunan aiki da cewa Gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta dauki dukkan matakin da ya kamata kan masu bujire wa umarninta.
Sassan da kwamitin ya ziyarta ciki har da garin Yankaysare da ke yankin karamar hukumar Dawakin Kudu, Kumbotso, Gezawa da karamar hukumar Nasarawa.