Gwamnatin Kano karkashin shirin ‘Appeals’ ta kulla yarjejeniya da makarantar harkokin noma ta Morocco domin neman taimakon yadda ake amfani da fasahar zamani wajen inganta noma.
Sauran bangarorin da aka rattabawa hannu kan yarjejeniyar sun hada da ingantawa tare da bayar da horo ga wadanda za su amfana da shirin, ma’aikata da sauran masu ruwa da tsaki da kuma harkar binkice da musayar tsare-tsare tsakanin bangarorin biyu.
A Lokacin bikin wanda aka gudanar ranar Litinin da ta gabata a makarantar ta Marocco, kwamishinan ma’aikatar gona da albarkatun ruwa na Jihar Kano, Dakta Yusuf Jibril Rirum wanda ya sa hannu a madadin gwamnatin Jihar Kano, yayin da shi kuma Farfesa Sa’id Amiri ya sanya hannu a madadin hukumar makarantar harkokin noman ta Marocco, dukkanin bangarorin biyu sun jaddada aniyarsu na ganin an samu nasarar aiwatar da yarjejeniyar, wanda aka gudanar a gaban jami’in shirin Appeals na kasa, Jobdi Muhammad.
Sauran wadanda suka shaida wannan biki sun hada da Manajan Daraktan Hukumar Noma da ci gaban Karkara (KNARDA), Dakta Junaid Yakubu, mashawarci na musamman ga gwamnan Kano kan harkokin noma, Alhaji Hafiz Muhammad, jami’in shirin Appeals na Kano, Dakta Hassan Ibrahim, daraktoci daga ma’aikatun noma da albarkatun kasa, wakilan shirin Appeals, jami’in shirin na kasa, masana da sauran masu ruwa da tsaki.