Gwamnatin Jihar Kano ta karyata rahoton bullar cutar kwalara a jihar.
Cibiyar Dakile da Cututtuka Masu Yaduwa ta Kasa (NCDC), ta ayyana Kano a cikin jihohi 31 da cutar ta barke.
- El-Rufai Ya Maka Majalisar Kaduna A Kotu Kan Zargin Karkatar Da Biliyan 432
- Yaƙi Da Ƙwaya: An Amince Wa NDLEA Siyo Manyan Makamai
Sai dai kakakin ma’aikatar lafiya ta Kano, Ibrahim Abdullahi, ya bayyana cewar cutar ba ta barke a jihar ba.
Ya ce, “A binciken da muka yi kawo yanzu babu cutar kwalara a Kano. Ba mu da ko mutum daya da ya kamu da cutar.
“Mun ga rahotannin a kafafen yada labarai amma babu ko mutum daya da ya kamu da cutar.”
Ya zuwa yanzu mutane 30 ne daga kananan hukumomi 96 a jihohi 30, aka tabbatar sun rasu, yayin da aka ruwaito cewar mutane 13 daga Kano sun kamu da cutar, sannan mutum daya ya rasu.
A cewar hukumar, ya zuwa yanzu, adadin wadanda suka mutu ya kai 34 yayin da aka tabbatar adadin wadanda suka kamu da cutar zuwa 1,288.