Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na bunkasa ilimi ga matasanta, inda ta yi shirin daukar karin dalibai 1,002 zuwa kasashen ketare, bayan nasarar daukar nauyin dalibai 1,001 a bara.
Mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya bayyana hakan a yayin ziyarar ban girma da tawagar kungiyar tarayyar turai (EU) suka kai gabanin bikin baje kolin karatu na 2025 na nahiyar turai a Kano.
- Sin Za Ta Ci Gaba Da Tabbatar Da Bunkasar Tattalin Arzikin Duniya
- Labarin Bukar, Malamin Da Ya Shafe Watanni 20 Ba Tare Da Albashi Ba A Borno
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Ibrahim Garba Shuaibu ya raba wa manema labarai, mataimakin gwamnan ya bayyana shirin a matsayin wata dama domin cike gibi ta yadda matasan Kano za su iya samun ilimi mai inganci tare da fafatawa da takwarorinsu na duniya.
Ya kuma kara da cewa, gwamnatin jihar Kano ta bai wa ilimi fifiko, wanda Kano ce a gaba wajen ware kasafin kudi mai yawa a shekarar 2024 da 2025 a fannin Ilimi. Bugu da kari, gwamnatin ta ayyana dokar ta-baci a fannin ilimi domin tabbatar da matasa sun samu ingantaccen ilimi wanda zai ba su damar yin fice a tsakanin takwarorinsu.
Da yake magana tun farko, Gautier Mignot, jakadan Tarayyar Turai a Nijeriya da ECOWAS, kuma jagoran tawagar, ya bayyana cewa, sun zo Kano ne domin halartar bikin baje kolin karatu na Turai da aka shirya yi a ranar 27 ga Fabrairu, 2025 a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp