Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da shirin fara aikin gyaran cibiyar fasa ta ‘Digital Industrial Park’ wadda aka lalata yayin zanga-zangar matsin rayuwa da aka gudanar ranar 1 ga watan Agustan 2024.Â
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya sanar da hakan a gidan gwamnatin Jihar Kano yayin ziyarar da ministan sadarwa da tattalin arziki, Dakta Bosun Tijjani ya kai masa a ranar Litinin.
- Gwamnatin Sakkwato Ta Kafa Kwamitin Da Zai Fara Sayar Da Kayan Abinci Masu Sauki
- Ban Ji Dadin Abin Da Libya Ta Yi Wa Super Eagles Ba – Tinubu
Mataimakin Gwamna Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda ya karbi bakuncin Ministan a madadin Gwamnan, ya jaddada kudirin gwamnatin na gaggauta gyara cibiyar don bunkasa harkokin fasahar sadarwa a jihar.
Gwarzo ya yi Allah-wadai da barnar da aka yi wa cibiyar, inda ya bayyana hakan a matsayin koma baya ga ci gaban Kano da Kanawa.
Ya kuma bayyana cewa Gwamnan ya umarci ma’aikatar ayyuka ta jihar da ta gudanar da cikakken bincike kan irin barnar da aka yi tare da fara aikin gyara nan take.