Majalisar Zartaswar Jihar Kano ta amince a kashe Naira Biliyan N40,353,117,070 domin aiwatar da wasu manyan ayyukan raya jihar da kuma inganta rayuwa.
Majalisar ta amince da haka ne a zamanta na 8, wanda aka yi a ranar Talata. Daga cikin ayyukan da gwamnatin za ta aiwatar akwai kashe Naira biliyan N15.97 domin gina Gadar Sama da Titin Ƙarƙashin Ƙasa a daidai Ƙofar Ɗan’agundi.
- Gwamnatin Kaduna Za Ta Sake Tsugunar Da ‘Yan Kudancin Jihar Da Suka Bar Matsugunansu
- Manzon Musamman Na Sin Kan Batun Yankin Gabas Ta Tsakiya Zai Halarci Taron Tallafin Jin Kai A Gaza
Za a kuma kashe Naira Biliyan N14.45 wajen gida Gadar Sama a Tal’udu.
Haka kuma, majalisar ta amince a kashe Naira biliyan N3.360 wajen gina rufaffiyar magudanar ruwa wadda za ta tashi daga Jakara-Kwarin Gogau, sai kuma Naira biliyan 1.579 da za a kashe wajen gina babban titi daga Ƙofar Waika zuwa Unguwar Daɓai zuwa Yankuje duk a cikin Ƙaramar Hukumar Gwale.
Haka nan kuma, a cikin sanarwar wadda Kwamishinan Yaɗa Labarai na Kano, Halilu Ɗantiye ya fitar, ta ce, an amince a kashe Naira biliyan N1.350 domin gina titin da ya tashi daga Unguwa Uku ‘Yan Awaki zuwa iyakar Limawa a Ƙaramar Hukumar Tarauni.
An ware Naira miliyan N820 domin ƙarasa aikin titin Kanye-Kabo-Dugabau a cikin Ƙaramar Hukumar Kabo.
An kuma sake ware Naira Miliyan N802 domin karasa aikin titin Ƙofar Dawaki zuwa Dandinshe zuwa Kwanar Madugu.
Akwai sauran ayyuka da dama waɗanda majalisar ta amince a fitar da kudi domin aiwatar da kyawawan Ayyuka.