A yau Asabar ne gwamnatin kasar Sin ta yi kakkausar suka da bayyana adawarta ga matakin Amurka na kakaba “harajin fito na ramuwar gayya.”
A cikin wata sanarwar da ta fitar, ta yi Allah-wadai da matakin na Amurka, wanda ya kasance daukar mataki bisa radin kai, da kuma kariyar cinikayya da cin zarafin tattalin arziki.
- Kasar Sin Za Ta Kara Sanya Harajin Fito Na Kaso 34% Kan Dukkan Kayayyakin Da Take Shigowa Daga Amurka
- Kofin Duniya: Kocin Nijeriya Na Fatan Matashin Ɗan Wasan Arsenal Nwaneri Ya Wakilci Ƙasar
Sanarwar ta kara da cewa, ta hanyar fakewa da abin da take kira “ramuwar gayya” da “adalci,” a zahiri dai Amurka ta tsunduma a aiwatar da dabarun danniya da babakere, tana neman cimma manufarta ta “Amurka na gaba da komai” da kuma “Amurka ta fi kowace kasa.” Har ila yau, Amurka na amfani da harajin fito don kawo cikas ga tsarin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa, tare da fifita muradun Amurka sama da moriyar bai daya ta duniya, tare kuma da sadaukar da halaltattun muradun kasashen duniya don cimma burin Amurka.
A ranar Laraba ne dai shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da wani sabon tsarin haraji, inda ya sanya mafi kankantar harajin fito kashi 10 cikin dari kan kayayyakin da ake shigowa da su daga dukkan kasashe abokan huldar cinikayyarta da kuma karin sama da hakan kan waasu kasashen. Bayan matakin na Amurka, a ranar Juma’a kasar Sin ta sanar da cewa, za ta sanya karin harajin fito kashi 34 cikin dari kan dukkan kayayyakin da ake shigowo da su daga Amurka daga ranar 10 ga watan Afrilu, wanda ya yi daidai da harajin fito na ramuwar gayya da Amurka ta kakaba kan kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin.
A cikin sanarwar da gwamnatin kasar Sin ta fitar yau Asabar ta ce, kasar Sin ta dauki kuma za ta ci gaba da daukar kwararan matakai don kiyaye ‘yancinta, da tsaro, da muradunta na samun ci gaba.
Ta kuma bukaci Amurka da ta daina amfani da harajin fito a matsayin makami don dakile ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, da kuma tauye hakkin samun halaltacciyar ci gaba na al’ummar Sinawa. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp