Gwamnatin kasar Sin ta tallafawa wasu iyalai marasa galihu da abinci a kasar Malawi. Rahotanni sun ce yawan garin masara da Sin ta baiwa kasar tallafi ya kai tan 33, wanda darajarsa ta kai dalar Amurka 24,650.
An mika tallafin ne ga gwamnatin Malawa a ranar Alhamis a birnin Lilongwe fadar mulkin kasar. Kafin hakan, kasar ta Sin ta mika wani tallafin na garin masara, da jan wake ga al’ummun gundumar Nkhotakota, wadanda darajarsa ta kai sama da dala 40,000.
- Samar Da Ababen More Rayuwa: Bankin Keystone Ya Jinjina Wa Gwamnan Zamfara
- Ya Kamata A Dakatar Da Duk Wasu Wasanni A Sifaniya Saboda Ambaliyar Balencia – Ancelotti
Yayin bikin mika tallafin na baya bayan nan, babban jami’in ofishin jakadancin Sin a kasar Wang Hao, ya ce hakan na nuni ga dangon zumunci dake tsakanin kasashen biyu.
A nasa tsokacin yayin da yake karbar tallafin, kwamishinan hukumar lura da bala’u a kasar Malawi Charles Kalemba, ya bayyana godiya bisa wannan tallafi na kasar Sin, yana mai cewa, Sin ta jima tana wanzar da kawance ta hanyar samar da tallafi mai muhimmanci, a yayin da Malawi ke cikin yanayi na matukar bukata.
Kalemba, ya kuma bayyana taimakon da Sin ke samarwa kasarsa a fannonin raya fasahohin noma da noman rani, a matsayin muhimman ginshikan cimma nasarar samar da abinci mai dorewa a Malawi. (Mai fassara: Saminu Alhassan)