Gwamnatin jihar Katsina ta ce ta dauki karin ma’aikata kusan 304 a hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar (KASROTA).
Babban Darakta na hukumar, Manjo Garba Yahaya-Rimi (Mai ritaya) ne ya bayyana hakan a ranar Lahadin a wata hira da ya yi da manema labarai a Katsina.
- Da Ɗumi-ɗumi: An Kashe Babban Kwamandan Sojoji A Katsina
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Mata Da Yara, Sun Kashe Mai Unguwa A Wani Sabon Hari A Katsina
Yahaya-Rimi ya ce, an dauki ma’aikatan ne domin karfafawa ma’aikatan hukumar kwarin guiwar yin aiki mai kyau wajen rage cin hanci da rashawa da masu amfani da tituna ke yi a jihar.
A cewarsa, daukar karin ma’aikata 304 ne domin karawa kokarin 96 da gwamnatin da ta gabata ta dauka.
Ya bayyana cewa sabbin ma’aikatan da aka dauka sun kammala horo kuma an tura su ne domin shiga rukunin farko wajen gudanar da aikin hukumar.
Shugaban hukumar KASROTA ya bayyana cewa hukumar ta yi shirin tabbatar da cewa jami’an kula da ababen hawan sun kasance a dukkanin kananan hukumomin jihar 34 domin tabbatar da bin doka da oda.
Yahaya-Rimi ya ce a yanzu haka ma’aikatan su na nan a fadin kananan hukumomi 13 daga cikin 34 na jihar, inda ya ce za a dauki karin ma’aikata da za su yi aiki da sauran wuraren.
Ya tunatar da masu amfani da hanyar cewa KASROTA ba a kafa ta a matsayin hanyar samun kudaden shiga ba, amma sai yi wa mutane hidima don tabbatar da tsaron rayukan jama’a da dukiyoyinsu.