Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya NFF, ta ce Katsina Football Academy ta samu damar wakiltar Nijeriya a gasar cin kofin Dana da za a yi a kasar Denmark.
Jami’in hulda da Jama’a na Flying Eagle’s, Sharif Abdallah, ne ya bayyana haka a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake zantawa da manema labarai a Katsina, inda ya ce makarantar ta samu gurbin shiga gasar ne saboda kwarewarta da kuma yadda take daukar kwallon matasa da muhimmanci, wanda hakan yasa makarantar horar da kwallon kafar ta Katsina ta samu damar wakiltar Nijeriya. cewar Sharif.
- Kungiyar Kwallon Kafa Ta Katsina United Na Neman Rangwami Akan Tarar Da Aka Yi Mata
- Rashin Tsaro: Gwamnatin Katsina Ta Kaddamar Da Matasa ‘Yan Sa-Kai
Sharif ya kuma bayar da tabbacin cewa NFF za ta ci gaba da tallafawa makarantar wadda ita ce irinta ta farko da take samun cikakken goyon bayan gwamnati
A nasa jawabin, kwamishinan matasa da wasanni na jihar, Alhaji Aliyu Lawal-Zakari, ya yabawa hukumar ta NFF bisa la’akari da yadda tasa makarantar ta wakilci Nijeriya.
Kwamishinan ya ce yana daya daga cikin manyan nasarorin da gwamnatin Gwamna Dikko Radda ta samu musamman kan ci gaban matasa, kuma wannan nasarar za ta ba wa daliban damar baje kolin basirarsu a matakin kasa da kasa a cewarsa.