Gwamnatin jihar Katsina ta kuduri aniyar ciyar da marasa karfi mutum miliyan 2,166,000 a cikin kwanaki 30 na watan Ramadan, wanda zai fara a yau.
Gwamnan jihar, Malam Dikko Umaru Radda ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da kwamitocin da ya dora wa alhakin kula da yadda za a yi rabon kayayyakin a matakin jiha da kananan hukumomi.
- Za Mu Iya Afmani Da Watan Ramadan Wajan Magance Matsalolin Da Muke Ciki – Fintiri
- Haduwa Da Mutanen Kirki Ita Ce Babbar Nasarata A Harkar Rubutu – Faridat Hussain
Gwamna Radda a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaransa, Ibrahim Kaula Muhammed, ya ce, shirin na da nufin ciyar da kimanin mutane 72,200 a kowace rana ta Ramadan, wanda jimillar ta kai kusan mutum miliyan 2,166,000 a tsawon watan Ramadan.
Tsarin da Gwamna Dikko Umar Radda ya sanar, ya hada da bayar da tallafin Naira N20,000 na ragi kan farashin masara, gero, da dawa kan kowane buhu, wanda hakan ya sa aka samu matukar ragi daga farashin da ake sayarwa a kasuwa. Sai dai, domin tabbatar da samun daidaito, gwamnatin ta yanke shawarar sayar da hatsin a kan loka goma ga kowane mai siye.