Gwamnatin Katsina za ta karfafa ci gaba da samar da kayan karatu ga manyan makarantun kiwon lafiya.
Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari shi ya sanar da hakan a lokacin bikin yaye daliba sama da 200 na kwalejin koyar da aikin jinya ta Kasim Kofar Bai da kwalejin koyar da aikin unguwar zoma ta Nana Babajo karo na 2 da ya gudana a kwalejin koyar da aikin unguwar zoma dabke Malumfashi.
Ya ce aikin gina tagwayen rukunin dakunan kwanan dalibai da yanzu haka ke gudana a kwalejin koyar da aikin unguwar zoma da ke Malumfashi da kuma daga darajar sashen kula da lafiyar yara zuwa dakin kwanan daliban a kwalejin koyar da aikin jinya ta Katsina na cikin kokarin da ake na sama wa daliban yanayi mai kyau.
Ya ce aikin daga darajar kwalejin zai taimaki daliban wajen ayyukan kiwon lafiya.
A lokacin da yake taya daliban da aka yayen murna, gwamna Masari ya yi fatan ganin ilimin da suka samu ya amfani al’umma.
Tun da farko, kwamishinan lafiyar Jihar Katsina, Yakubu Nuhu Danja ya yi nuni da cewa zamanantarwa da kuma daga darajar karin manyan asibitoci da gwamnatin Jihar Katsina ta yi zai bunkasa ayyukansu. Sannan ya yaba wa gwamnatin Jihar Katsina bisa ba da kwangilar gina rukunin kwanan daliban 2 da za su iya daukan dalibai 300 a kwalejin.