Gwamnatin Kebbi ta bayar da kwangilar Naira Biliyan 3.8 don sake gyaran titunan garin Yauri da ke masarautar Yauri a jihar.
Wannan dai ya yi daidai da shirin sabunta birane na Gwamna Nasir Idris wanda zai kai ga dukkan babban birnin jihar Kebbi, da Hedikwatar Masarautu hudu da kuma hedikwatar kananan hukumomi 21 na jihar.
- Shin Wasan Kwaikwayon Na Zaben Kakakin Majalisar Wakilan Amurka Ta Kawo Karshe Ne?
- An Bude Iyakar Rafah Ga Wasu ‘Yan Kasashen Waje A Karon Farko
Kwamishinan Ayyuka da Sufuri, Alhaji Abdullahi Umar-Faruk ne ya bayyana hakan a Birnin Kebbi, a yayin da yake rattaba hannu kan yarjejeniyar kwangilar da wani kamfanin gine-gine na kasar Sin, China Zhounghou Nigeria Limited.
Ya kara da cewa, “A yau, bisa tsarin shugabanci nagari na gwamnatin Gwamna Nasir Idris, mun taru ne domin shaida wata babbar nasara a tsakanin mutane da yawa masu zuwa, wato bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar kwangila tsakanin gwamnatin jihar da Kamfanin kasar Sin Zhounghou. Nigeria Limited.
“kwangilar gyaran titunan garin Yauri ne, wanda ya hada da gyara da kuma sake gina wasu hanyoyi guda hudu da suka hada da, karamar hukumar Dawanau, titin kasuwa da ke kusa da Tashar Garkuwa, mahadar Garkan Dudu-Laberiya da ofishin ‘yansanda – Bankin Union baki daya. Za a kashe Naira Biliyan 3.8,” inji shi.
A cewarsa, kwangilar za ta shafe kusan kilomita 5.2.
“A cikin watan Agusta, Gwamna Idris ya sake yin wata gagarumar nasara wajen bayar da kwangilar kammala ginin sakatariyar zamani a kan kudi Naira biliyan 10.5,” in ji shi.
“Muna kuma fatan kara tabbatar da cewa ma’aikatar ba za ta bar wani abu ba wajen tabbatar da cewa an kiyaye mafi ingancin aiki a tsawon watanni 18,” kwamishinan ya tabbatar.
Mista Wei Meng, wakilin kamfanin China Construction Company, China Zhounghou Nigeria Limited a takaice, ya tabbatar da cewa, kamfanin zai bi yarjejeniyar kwangila da kuma tabbatar da ingantaccen aiki.