Gwamnatin Jihar Legas ta bayar da hutu ga ma’aikatan gwamnati a jihar domin su samu damar zuwa karbar katin zabe.
A cewar sanarwar da shugaban ma’aikatan jihar, Hakeem Muri-Okunola, ya fitar a ranar Alhamis, ya ce, an tsara yadda ma’aikata daban-daban za su karbi katinansu a ranakun da aka kebe.
- Liu He Ya Tattauna Da Sakatariyar baitulmalin Amurka
- Mutum Daya Ya Mutu Bayan Da Gini Ya Rufta Masa A Legas
Ya ce, “Bisa kara wa’adin karbar katin zabe da hukumar zabe mai zaman kanta ta yi, kan hakan ana sanar da ma’aikatan gwamnati da ba su karbi katinan zabensu ba a wuraren da INEC ta ware da su karba kafin ranar Lahadi 29 ga watan Janairu 2023 domin samun damar zaben wadanda suke so.
“Gwamna ya amince da ware ranaku domin bai wa ma’aikatan gwamnati damar karbar katin a kananan hukumominsu ko yankunansu.”
Shugaban ma’aikatan ya kara da cewa ranakun da aka ware a matsayin na hutun karbar katin sun hada da ranar 24 ga watan Janairu, 2023 ga ma’aikatan.
INEC ta sanar da karin kwanaki don bai wadanda ba su samu damar karbar katin zaben ba da su karba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp