Akalla mutum guda ne aka tabbatar da mutuwarsa bayan da wani gini ya rufta a yankin Aromire da ke Ikeja a Jihar Legas.
Wakilin LEADERSHIP, ya gano cewa lamarin ya faru ne da karfe 6:35 na yammacin ranar Laraba.
- Mu’amala A Tsakanin Sin Da Manyan Kasashen Duniya A Shekarar 2022
- Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Dangane Da Yunkurinta Na Toshe Kofofin Wasu Kasashe Na Samun Ci Gaba
Babban Sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Legas, (LASEMA), Dakta Olufemi Oke-Osanyitolu, ne ya sanar da hakan ta cikin sanarwar da ya fitar.
Ya ce, ginin bene mallakin Kilms Mary ne da wasu baragurbin lebururi suka gina bisa rashin kwarewa da hakan ya janyo rushewarsa.
Ya ce, “Hukumarmu ta samu kirar waya kuma cikin hanzari jami’anmu suka isa wajen, mun gano an gina wajen ne bisa rashin kwarewa.
“Wani babban mutum da aka ce yana aikin Walda ne ya rasa rayuwarsa nan take.”
Ya ce, tuni suka fara gudanar da bincike tare da ‘yan sanda domin gano wasu bayanai kan ginin da musabbin rushewarsa.