Wani kasurgumin shugaban ‘yan bindiga, Bello Turji, da ke ta’addanci a arewacin Nijeriya, ya zargi karamin ministan tsaro kuma tsohon Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, da rashin kula da lamarin sulhu da ‘yan bindiga yadda ya kamata a lokacin da yake gwamnan jihar.
A lokacin da yake gwamna, Matawalle ya kaddamar da shirin yin afuwa ga ‘yan bindiga inda ya bayyana tattaunawa a matsayin mafi kyawun zabi na magance ta’addancin ‘yan bindiga.
- Jihar Kano Na Shirin Gudanar Da Zaben Ƙananan Hukumomi – Gwamna Abba
- Shugaba Tinubu Ya Mika Sakon Ta’aziyya ga Kasar Vietnam Kan Rasuwar Nguyễn Phú Trọng
Sai dai kuma daga baya ya janye afuwar, yana mai cewa ‘yan bindigar sun gaza rungumar shirin zaman lafiyar da gwamnatinsa ta yi musu.
A cikin wani faifan bidiyo da aka saki a shafukan sada zumunta kuma Daily Trust ta nakalto, Turji ya alakanta karuwar ta’addanci a Zamfara da sauran jihohin Arewa maso Yamma kan manufofin da Matawalle ya tsara a lokacin da yake gwamna.
“Duk mutumin da ke zaune a Shinkafi, Zurmi, da Isa (Jihar Sokoto) ba zai iya musanta wannan ikirari ba. Akwai wasu gungun ‘yan bindiga da suka zama ‘yan lelen tsohon gwamnan. Na kore su daga Shinkafi, na kashe shugabansu, Dudu, domin samun dawwamammen zaman lafiya a Shinkafi. Kungiyar na da makamai 200, amma daga baya gwamnan ya karbe su (Yaran Dudu) a gidan gwamnati.
“Kuma gwamnati ta gaza nemansu (Yaran Dudu) da su mika makamansu. Sannan akwai Wata kungiya da Bashari Maniya ke jagoranta tana da bindigogi sama da 300.”
Turji ya yi ikirarin cewa, ya kwace bindigu 30 daga hannun sansanin ‘yan bindigar da ke karkashin jagorancin Bashari Maniya, kuma kungiyar ba ta taba mika makamanta ga gwamnati ba.
A cikin faifan bidiyon, Turji ya kuma yi zargin cewa, wasu shugabannin kungiyoyin ‘yan bindiga da ke cikin yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin Matawalle ta kaddamar sun koma Sokoto da zama bayan sun bai wa yaransu makamai domin ci gaba da yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.
“Ali yaro ne ga Kabiru Maniya, kuma shi ne ke da alhakin kai hare-hare a yankin Tangaza. Bashiri da Kabiru duk suna zaune ne a cikin babban birnin Sokoto, suna jin dadin rayuwarsu. Akwai Wani Buhari, shi ma yana cikin garin Sokoto yana jin dadin rayuwarsa.
“Makonni uku da suka wuce, an kama wani kanin Buhari da bindigogi a cikin babban birnin Sokoto. Babu mai musanta wannan. Zan iya fitowa da hujjojin bidiyo wanda ke nuna yadda Kabiru Maniya ke harba manyan bindigogi.
“Abin tambaya a yanzu shi ne, ina bindigoginsu bayan da suka ce sun rungumi zaman lafiya sun zauna a garin Sokoto?
Ya dace gwamnati ta bayyana wa ’yan Nijeriya wanda ke da alhakin kashe jama’a. Su daina zargin Bello Turji da kashe-kashe da garkuwa da mutane.
“Mutanen da ake garkuwa da su a cikin babban birnin Sokoto aka kai su bayan Achida da Goronyo, wa ke da alhakin yin garkuwa da su? Har yanzu Bello Turji ne ? Wanda yake zaune lafiya a Shinkafi?
Kokarin jin ta bakin Matawalle domin jin ta bakinsa ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Kiraye-kiraye da yawa da aka yi wa Henshaw Ogubike, mai magana da yawun ma’aikatar tsaro, ya ci tura.
Ogbuike, ya aika da sakon tes, inda ya nemi wakilin Daily trust ya yi masa bayanin kiran ta hanyar rubutu (tes) amma bai mayar da martani ga sakon da aka aika masa ba har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton.
A baya dai Matawalle ya musanta alaka da ‘yan bindigar, ya kuma kara da cewa, gwamnatinsa ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin ta magance matsalolin tsaro a Zamfara a lokacin da yake kan mulki.