Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya amince da daukar karin malamai 550 a jihar tare da gargadi da jan kunne ga hukumar kula da ayyukan malamai kan son zuciya.
Sule ya yi wannan gargadin ne a lokacin da yake bude taron kwana uku ga shugabannin makarantun sakandire na jihar a ranar Laraba a garin Lafiya, inda ya ce wadanda suka cancanta kuma kwararru kawai ake dauka aikin karantarwa a jihar.
Daily trust ta ruwaito cewa an dakatar da tsohon shugaban hukumar kula da ayyukan Malamai ne saboda sakaci da yadda aka gudanar da aikin daukar malamai 400 na baya-bayan nan.
“Ba zan amince da duk wani jerin sunayen da aka kawo su gabana ba dake dauke da sunayen ’yan uwa da abokan arziki. Ina son kwararrun malamai Kawai, ba wai ‘ya’yan mowa ba Kadai,” inji Gwamnan.
A baya dai jihar a lokacin mulkin tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Umaru Tanko Al-makura ta dauki malamai sama da 2,000 sannan gwamnati mai ci yanzun ta dauki malamai 400.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp