Gwamnatin jihar Nasarawa ta ce, ta cafke mutane 69 bisa samunsu da laifin karya dokokin tsaftace muhalli na jihar.
Kwamishinan muhalli da albarkatun ƙasa na jihar, Hon. Yakubu Kwanta, shi ne ya shaida hakan a lokacin da ke ganawa da manema labarai kan aikin tsaftace muhalli na ƙarshen wata da ya gudana a Lafia.
- Za A Kammala Aikin Bututun Iskar Gas Na AKK A Disambar 2024 – NNPC
- Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Tattauna Da Masana Tsara Manufofi Da ’Yan Kasuwa Na Amurka
A cewar kwamishinan, masu aikata laifukan waɗanda mafi yawansu matuƙa motoci, mashina mai ƙafa uku, da babura ne, tawagar tabbatar da bin dokokin tsaftace muhalli ne suka kama su a sassa daban-daban na ƙananan hukumomi 13 da suke faɗin jihar yayin aikin tsaftace muhallin.
Kwamishinan ya ƙara da cewa, waɗanda aka kaman sun karya tanadin sashi na 9 (2) na dokar muhalli ta jihar bisa laifin zirga-zirga a lokacin da aikin tsaftace muhallin ke gudana.
Kwamishinan ya kuma ƙara da cewa, jihar ta ɓullo da wasu sabbin dabarun sanya ido a yayin da ake aikin tsaftace muhalli ta hanyar kafa wata tawaga ta musamman na wasu mutane da za su ke yin basaja suna shiga cikin wurare domin sanya ido domin ganin an tursasa jama’a rungumar ɗabi’ar bin dokokin tsaftace muhallin.
Yayin da ya ke gargaɗin tawagar masu sanya ido kan duk wani yunkurin nau’in zagon ƙasa ga aikin, Malam Kwanta, ya buƙaci jama’a da su rungumi ɗabi’ar tsaftace muhalli domin kariya daga ɓarkewar cutuka a faɗin jihar.