Gwamnatin Jihar Nasarawa ta fara sabunta asibitoci 58 domin inganta kula da lafiya a matakin farko.
Wannan aiki na gudana ne ƙarƙashin Hukumar Ci Gaban Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar (NAPHDA), tare da haɗin gwiwar Bankin Duniya da sauran abokan hulɗa.
- Fashewar Tankar Man Fetur: Rundunar ‘Yansanda Ta Tabbatar Da Mutuwar Mutane 6, Motoci 14 Sun Kone A Abuja.
- Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 84, Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 3 A Katsina
Shugaban hukumar, Dokts Usman Saleh, ya bayyana hakan a lokacin da yake karɓar baƙuncin ƙungiyar manema labarai a Lafia.
Ya ce sabunta asibitocin zai taimaka wajen samar da ingantaccen kulawar lafiya ga jama’a tare da rage kuɗin da ake kashewa wajen neman lafiya.
Ya ƙara da cewa ana sa ran kammala aikin kafin kars6hen watan Yuni, sannan an shirya tabbatar da cewa dukkanin gundumomi 147 na jihar suna da asibiti ɗaya da ke aiki dare da rana.
Dokta Saleh ya yaba wa Gwamna Abdullahi Sule bisa jajircewarsa wajen bunƙasa fannin kiwon lafiya a jihar, yana mai cewa gwamnan na ƙoƙarin tabbatar da cewa kowa yana samun ingantaccen kulawar lafiya.
Har ila yau, a buƙaci a samu haɗin gwiwa da manema labarai da sauran masu ruwa da tsaki domin wayar da kan jama’a kan muhimmancin kula da lafiya da zuwa asibiti don bincike da magani.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp