Gwamnatin Jihar Nasarawa ta yi gargadin cewa za ta tushe gine-ginen da aka yi ba bisa ka’ida ba a kan hanyoyin wucewar ruwa a kokarinta na dakile aukuwar ambaliyar ruwa a jihar.
Kwamishinan muhalli na jihar, Malam Yakubu Kwanta, shi ne ya shaida hakan a hirarsa da ‘yan jarida bayan kammala aikin tsaftace muhalli na wata-wata da aka gudanar jiya a Lafia.
A kwanakin baya ne dai hukumar NiMET ta yi hasashen cewa za a samu ambaliyar ruwa a jihohi 25 ciki har da Nasarawa.
Da ya ke samun wakilcin Malam Abubakar Mohammed, babban jami’in kula da muhalli wanda kuma shi ne babban jami’in gurfanar da masu laifi na ma’aikatar, ya ce, tun lokacin da suka samu bayanin akwai yiyuwar ambaliyar suka nusar da mutanen da suke zaune a yankunan da abun ya shafa domin su zama cikin shiri tare da shirye-shiryen kaura zuwa wasu wuraren domin kare rayuka da dukiyarsu.
Ya ce, baya ha matakan gwamnati ke dauka na ganin ba a samu ambaliyar ba, su ma mutane da bukatar su bada nasu gudunmawar wajen biyayya wa matakan da gwamnati take dauka.
Kan hakan ya ce dukkanin gidajen da aka yi a kan hanyoyin ruwa dole ne a rushesu domin bai wa ruwa hanyar da zai wuce ba tare ya janyo wata barna ba kamar shekarar da ta faru a gabata ba.
A kalla mutum 400,000 ne suka yi gudun hijira a kananan hukumomin 11 cikin 14 da suke jihar a shekarar da ta gabata sakamakon ambaliyar ruwa.
Daga cikin ayyukan akwai Awe, Toto, Keana, Doma, Nassarawa Keffi, Nasarawa Eggon, Obi, Lafia, Wamba da Karu.
“Idan kuka rufe wa ruwa hanyarsa da hana masa wucewa, kai tsaye kuna gayyatar annobar ambaliya ne, saboda ko ma ta ya ya ne dole ruwa zai nema wa kansa hanyar wucewa,” Kwanta ya shaida.