A cikin tsare-tsarenta na kasafin 2023, gwamnatin jihar Neja ta dage takunkumin daukar ma’aikata, inda ta shirya daukar sabbin ma’aikata har 3,000.
Gwamnatin ta ware naira biliyan 3 a cikin kasafin kudin bana domin biyan albashin sabbin ma’aikatan da za ta dauka da aka yi harsashen samun karin kudin albashin wata-wata na miliyan 300.
- Hukumar Lafiya Ta Ankarar Da Al’ummar Jihar Neja Kan Cutar Bakon Dauro
- Mutane Da Dama Sun Mutu A Wata Arangama Tsakanin ‘Yan Bindiga Da ‘Yan Banga A Neja
Kwamishinan tsare-tsare na jihar, Malam Zakari Abubakar, ya bayyana hakan a karshen mako ce wa gwamnan Jihar, Alhaji Abubakar Sani Bello ya gabatar da kasafin a zauren Majalisar Dokokin Jihar.
Zakari ya yi bayanin cewa wannan matakin na daga cikin kokarin Gwamnatin jihar na samar da aikin yi ga dumbin matasa a jihar.
Ya kara da ce wa tunin shirye-shiryen daukar ma’aikatan ya fara kankama. Ya ce, “Gwamnati ta dukufa wajen shawo kan matsalar rashin aikin yi a fadin jihar sannan wannan dalilin ne ya sanya aka sanya daukar sabbin ma’aikata a cikin kasafin kudi na shekara mai zuwa.”
Kwamishinan ya ce, kasafin na badi an tsara shi ne da zimmar karasa ayyukan da ake yi domin ganin jama’a na ci gaba da samun rayuwa mai inganci.
Ya kara da cewa a kasafin an ware N91.044, 745, 351.31 kwatankwacin kaso 38.11 cikin dari ga sashin ayyukan yau da kullum da kuma ware naira biliyan N147, 879, 712, 431, 16 kwatankwacin kaso 61.89 na kasafin wajen gudanar da manyan ayyuka.