Gwamnatin janhuriyar Nijar, ta yaye tsofaffin mayaka 369 da aka yi wa horon sauya tunani bayan sun amince su ajiye makamai. An gudanar da bikin yaye mutanen ne a ranar Litinin, a cibiyar horo da sauya tunani ta Hamdallaye dake yammacin kasar.
Cikin wadanda aka bai wa horon akwai maza 307, da mata 21 da kuma yara kanana 41. Bayan kammala bikin yaye su, an mika musu kayayyakin gudanar da sana’o’i, domin taimaka musu komawa rayuwar yau da kullum cikin al’umma.
Ma’aikatar ayyukan cikin gida ta kasar ce ta shirya bikin, a wani bangare da shirin kasar na kwance damara, da sauya tunani, da sake mayar da wadanda suka taba shiga kungiyoyin ta da kayar baya cikin al’umma.
A ta bakin shugaban bikin, kuma gwamnan Jihar Tillabery Maina Boukar, taron na wannan karo ya shaida aniyar gwamnatin Nijar, ta bai wa wadanda suka rungumi shirin ajiye makamai damar sauya rayuwarsu, da taimaka musu wajen cimma nasarar komawa cikin al’umma cikin mutunci.
Boukar ya ce, “Wannan muhimmin zabi, ya nuna aniyar gwamnatin Nijar ta kare ikon mulkin kai, da wanzar da tsaro, da tabbatar da zaman lafiya karkashin kyawawan manufofin kasa, ba tare da dogaro ga wasu ajandoji daga ketare ba.”