Fadar shugaban Nijeriya ta yi fatali da wani rahoto da kungiyar Tarayyar Turai, EU, ta fitar da ya ce akwai kura-kurai kan zaben kasar na 2023.
An gudanar da zaben shugaban kasar ne a watan Fabrairu inda hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya, INEC, ta ayyana dan takarar jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara.
- Tinubu Ya Koma Abuja Bayan Ziyarar Faransa, Landan Da Legas
- Kada Ka Nada Tsohon Gwamna Mukamin Minista -Kungiya Ga Tinubu
TRT Afrika ta rawaito cewa, a rahoton da jagoran kungiyar Tarayyar Turai Barry Andrews ya fitar ya ce an tafka kura-kurai a zaben don haka ba shi da sahihancin da ya kamata.
Amma a wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Mr Dele Alake ya fitar ranar Lahadi, ya yi watsi da rahoton Tarayyar Turan yana mai cewa ya nuna son kai karara.
Mr Alake ya ce da ma tun a watan Mayu suka sanar da ‘yan Nijeriya cewa wata kungiya na shirin fitar da rahoto da zummar bayyana zaben kasar a matsayin gurbatacce.
“Yanzu tun da wannan kungiya ta fitar da abin da ta yi ikirarin cewa shi ne rahotonta na karshe, muna iya sanar da ‘yan Nijeriya da duniya cewa muna sane da tuggun Tarayyar Turai na jaddada son kai da ikirarinta mara tushe kan sakamakon zaben,” in ji kakakin shugaban kasar.
Ya kara da cewa abin takaici ne yadda Tarayyar Turai, wadda ta tura masu sanya ido da ba su kai 50 ba a kasa mai akwatunan zabe fiye da 176,000, ta fito tana cewa zaben kasar bai inganta ba.
“Muna so mu sani sannan mu tambayi EU, ta yaya ta hada rahotonta na karshe bayan kuwa masu sanya idanunta a zaben kalilan ne wadanda, babu shakka, sun dogara ne da jita-jita da wane-ya-ji-ga-wane da masu sharhi a soshiyal midiya da ba su da masaniya da kuma masu magana da yawun ‘yan hamayya,” a cewar sanarwar.