Gwamantin Jihar Osun ta ce, ta bankado tulin basukan da ya kai na Naira biliyan 76 na albashi, fansho da alkawuran da suka shafi Inshora da gwamantin baya a karkashin gwamantin Gboyega Oyetola.
Babban Sakataren ma’aikatar kudi ta jihar, Misis Bimpe Ogunlumade, ce ta shaida hakan a ranar Alhamis a hirarta da ‘yan jarida dangane da bayanin halin da lalitar jihar ke ciki.
- Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Yanke Wa Dan Takarar Gwamnan YPP Hukuncin Daurin Shekaru 42 A Akwa Ibom
- Sharuddan Da APC Ta Gindaya Kafin Tinubu Ya Halarci Taron Muhawarar Shugabancin Kasa
Bayanin gwamnatin jihar ya yi hannun riga da ikirarin gwamnatin baya ta Oyetola da ya ce ya bar jihar da zunzuturun kudi har Naira biliyan 14 ga sabuwar gwamnatin Gwamna Ademola Adeleke, da wasu bayanai da ya yi, inda kuma iya gwamnatin ta ce, ta gano duk karya ce kawai.
A wata sanarwar da kakakin gwamnan Osun, Mallam Olawale Rasheed, ya fitar, ya ce, wannan adadin bashi ne zallar basukan da gwamnatin baya ta bar musu ba, inda ya ce zuwa gobe za su fitar da cikakken bayani kan basukan da gwamnatin baya ya arce ta bar su da su.