Gwamnatin Sakkwato da hadin guiwar Sanata Aliyu Wamakko, sun ba da gudunmuwar naira miliyan 16.6 ga mutane 66 da sojoji suka ceto daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su.Â
Gwamna Aliyu, da yake jawabi a wajen taron, ya bayyana nasarar ga hukumomin tsaro da ke fadi tashi tare da goyon bayan gwamnatin jiha domin kawar da ayyukan ta’addanci a fadin jihar.
- Kasar Sin Ta Ware Yuan Miliyan 400 Don Taimakawa Wadanda Bala’in Girgizar Kasa Ta Shafa A Gansu Da Qinghai
- Zaben Cike Gurbi: APC Za Ta Sayar Da Takardar Tsayawa Takarar Sanata Naira Miliyan 20
“Wannan muhimmiyar rana ce a matakin da muka dauka na yaki da ayyukan ta’addanci wanda babba ne a cikin ajandoji tara da muke da su na bunkasa jihar Sakkwato. Muna taya shugabannin hukumomin tsaro murnar ceto wadannan mutane daga masu garkuwa da su.” In ji shi.
Ya bayyana cewar kowane daga cikin mutanen likitoci sun yi musu gwaje-gwaje domin tabbatar da lafiyarsu, haka kowane zai samu buhun shinkafa, masara, gero da kuma naira dubu 100 daga gwamnatin jiha.
Da yake kaddamar da tallafin, Sanata Aliyu Wamakko da ke wakiltar Sakkwato ta Arewa a Majalisar Dattawa ya bayar da tallafin naira miliyan 10 ga mutanen tare da yaba wa kokarin Gwamnan da kuma taya mutanen murna kan samun ‘yanci da suka yi.
Jami’in sojan da ya jagoranci ceto mutanen, kuma Kwamanda na runduna ta 8 da ke Sakkwato, Birgediya Janar Alex Tawasimi ya bayyana jin dadinsa kan gudunmuwar da gwamnatin jiha ke bai wa jami’in tsaro a Jihar.
Lami Tsalha da Sulaiman S/Noma a madadin wadanda aka ceto sun gode wa gwamnan da Sanata Wamakko da jami’in tsaro da suka jajirce suka ceto su a hannun wadanda suka yi garkuwa da su.