Yau Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning ta gudanar da taron manema labarai na yau da kullun.
Dangane da zargin da Amurka ta yi wa wani kamfanin Sin na bayar da tallafin fasaha ga ayyukan sojojin Sin kan wasu wurare a cikin Amurka, Mao Ning ta bayyana cewa gwamnatin Sin tana mai da hankali da kuma kare sirrin bayanai da tsaronsu bisa doka, kuma ba ta taba bukatar kamfanoni su tattara ko adana bayanai ba bisa ka’ida ba, kuma ba za ta yi hakan a nan gaba ba.
Dangane da batun shugaban Amurka Donald Trump ya taba yi cewa yana iya amincewa da shirin kakaba takumkumi ga kasashen dake hulda da Rasha, Mao Ning ta bayyana cewa Sin za ta ci gaba da adawa da takunkumi da ake kakabawa daga bangare daya ba tare da wani tushe a cikin dokokin kasa da kasa, ko izini daga kwamitin tsaron MDD ba.
Kazalika, a kan batun katobarar da firaministar Japan Takaichi Sanae ta yi game da Taiwan, Mao Ning ta ce kalamanta sun bata wa jama’ar Sin rai sosai kuma sun illata yanayin mu’amalar jama’a tsakanin Sin da Japan. Ya kamata Japan ta bi ruhin takardu hudu na siyasa tsakanin Sin da Japan, ta janye katobara da kuskuren da ta tafka nan take, sannan ta hana kara tabarbarewar dangantakar Sin da Japan.
Bugu da kari, Mao Ning ta bayyana cewa firaministan Sin Li Qiang ba shi da shirin ganawa da shugabannin Japan a lokacin da yake halartar taron kolin shugabannin G20 da za a yi a Johannesburg dake Afirka ta Kudu.(Safiyah Ma)













