• English
  • Business News
Tuesday, August 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tarayya Da Kasar Faransa Sun Sake Sabunta Yarjeniyar Farfado Da Hakar Ma’adanai

by Abubakar Abba and Sulaiman
7 months ago
in Tattalin Arziki
0
Gwamnatin Tarayya Da Kasar Faransa Sun Sake Sabunta Yarjeniyar Farfado Da Hakar Ma’adanai
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Nijeriya da kasar Faransa sun sake sabunta jarjeniyar da suka rattabawa hannu a a watan ga ya gabata a kasar Fasris, bisa tabbatar da cewa, kasar ta Faransa, na daga darajar cibiyoyin yin gwaje-gwaje, samar da kayan aiki na fasahar kimiyya da kuma zuba kudade, domin a farfado da bangaren tasawirar adana bayanai ta Hukumar Gudanar Da Binciken Tasawirar Kasa NGSA.

An dauki wannan matakin ne, bayan wata ganawa da aka yi a tsakanin Ministan Bunkasa Hakar Ma’adanan Kasa Dakta Dele Alake da kuma wata tawagar samar da tsare-tsaren Ma’adanai na kasar Faransa wadda Benjamin Gallezot, ya jagoranta.

  • Fatara Da Talauci Na Yi Wa ‘Yan Nijeriya Miliyan 13 Barazanar Fadawa Kangin Talauci A 2025 — Rahoto
  • Tsohon Shugaban Google: Deepseek Ya Kawo Muhimmin Sauyi A Bangaren AI

Sun tattauna ne, a tare da sauran tawagarsu, a bayan fagen taron da ake ci gaba da gudanwarwa a birnin Riyadh na kasar Saudi Arabiya kan makomar Ma’adanan Kasa a karkashin Kungiyar Ma’adanan Kasa.

A cikin sanarwar da mai bai wa Ministan Bunkasa Hakar Ma’adanai Dakta Dele Alake shawara ta musamman Kehinde Bamigbetan, ya rabawa manema labarai a ranar Litinin, Ma’aikatun biyu sun amince da yin musayar bayanai, kan dokokin Ma’adanan kasa na kasashen biyu, domin yin nazari kan dokoki, musamman kan yadda za a magance hakar Ma’adanai ta haramtaciyar hanya.

Sanarwar ta ce, Gallezot ya ayyana cewa, sashensa zai tantance jeren sunayen Kamfaonin kasar Faransa, da suka sha’awarsu, ta zuba hannun jari a cikin fannin hadakar Ma’adanai na Nijeriya tare da kuma mikawa Ma’aikatar hakar Ma’adanan Kasa ta Nijeriya, sunayen ga Bunkasa Hakar Ma’adanai ta Nijeriya.

Labarai Masu Nasaba

NBS Ta Bayyana Dalilin Raguwar Farashin Kaya A Nijeriya

Masu Ruwa Da Tsaki Sun Bukaci Bunkasa Fannin Mai Da Ake Hakowa A Teku

A na sa jawabin Ministan Bunkasa Hakar Ma’adanai Dakta Dele Alake, ya godewa Gallezot, kan yin aikin da ya yi dashi, wajen tabbatar da rattaba hannun wannan yarjejeniyar, duk da karancin lokacin da ake dashi na lokacin da yake da shi, a lokacin da Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ziyarci Shugaban kasa Bola Tinubu.

Adeleke ya yi nuni da cewa, sake sabunta wannan yarjejeniyar ta kawo karshen yunkurin ‘yan adawar siyasa na kasar nan, kan yunkurinsu na gayawa ‘yan Nijeriya bayanan karya kan manufar wannan yarjejeniyar.

Ministan ya ci gaba da cewa, Kungiyar ta Makomar Ma’adanan Kasa, za ta bai wa kasashen biyu damar fahimtar yadda za a samar da tsare-tsare da dabaru da kuma ayyukan da ya kamata ayi, domin a cire dukkanin wani kwankwato da ake da shi, musamman domin a samar da samakon da ya kamata.

Shi kuwa Farfesa Olusegun Ige, Darakta Janar na Hukumar ta NGSA ya sanar da burin Hukumarsa na son samun kayan kimiyyar zaman, domin ta kara bunkasa ayyukanta, inda ya yi nuni da cewa, rashin samun kayan aikin na fasahar zamani, na janyo jinkiri wajen gudanar da ayyukan hakara Ma’adanai masu dimbin yawa a kasar nan.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Gwamnatin Kano Za Ta Kashe N2.5bn A Auren Gata

Next Post

Yawan Fasinjojin Da Jiragen Kasa Suka Dauka Ya Zarce Miliyan 200 A Lokacin Bikin Bazara A Kasar Sin

Related

NBS Ta Bayyana Dalilin Raguwar Farashin Kaya A Nijeriya
Tattalin Arziki

NBS Ta Bayyana Dalilin Raguwar Farashin Kaya A Nijeriya

4 days ago
Masu Ruwa Da Tsaki Sun Bukaci Bunkasa Fannin Mai Da Ake Hakowa A Teku
Tattalin Arziki

Masu Ruwa Da Tsaki Sun Bukaci Bunkasa Fannin Mai Da Ake Hakowa A Teku

4 days ago
Dalilin Da Ya Sa Gwamnatin Jihar Kuros Ribas Ta Yi Hadaka Da Hukumar NPA
Tattalin Arziki

Dalilin Da Ya Sa Gwamnatin Jihar Kuros Ribas Ta Yi Hadaka Da Hukumar NPA

4 days ago
Ma’aikatan Sufurin Jiregen Sama Sun Bukaci Tinubu Ya Janye Shirin Sayar Da Filayen Jiragen Sama
Tattalin Arziki

Ma’aikatan Sufurin Jiregen Sama Sun Bukaci Tinubu Ya Janye Shirin Sayar Da Filayen Jiragen Sama

2 weeks ago
NPA Ta Fito Da Sabuwar Doka Kan Kayan Da Ake Ajiyewa A Tashoshinta
Tattalin Arziki

NPA Ta Fito Da Sabuwar Doka Kan Kayan Da Ake Ajiyewa A Tashoshinta

2 weeks ago
Shirin Iskar Gas Na CNG Abin A Yaba Wa Shugaba Tinubu Ne -Shugaban IPMAN Na Ƙasa
Tattalin Arziki

Shirin Iskar Gas Na CNG Abin A Yaba Wa Shugaba Tinubu Ne -Shugaban IPMAN Na Ƙasa

2 weeks ago
Next Post
Yawan Fasinjojin Da Jiragen Kasa Suka Dauka Ya Zarce Miliyan 200 A Lokacin Bikin Bazara A Kasar Sin

Yawan Fasinjojin Da Jiragen Kasa Suka Dauka Ya Zarce Miliyan 200 A Lokacin Bikin Bazara A Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

Ranar Hausa Ta Duniya: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka

Ranar Hausa Ta Duniya: Ba Ka Iyawa Duk Dagewarka Kuma Ba A Yaba Maka

August 26, 2025
Ɗan Nijeriya Ya Lashe Lambar Azurfa A Gasar Ninkaya Ta Duniya

Ɗan Nijeriya Ya Lashe Lambar Azurfa A Gasar Ninkaya Ta Duniya

August 26, 2025
Ranar Hausa: Yadda Hausawa Ke Tunƙaho Da Harshensu A Faɗin Duniya

Ranar Hausa: Yadda Hausawa Ke Tunƙaho Da Harshensu A Faɗin Duniya

August 26, 2025
An Yi Bikin Mu’ammalar Al’Adu Na SCO Na 2025 A Beijing

An Yi Bikin Mu’ammalar Al’Adu Na SCO Na 2025 A Beijing

August 25, 2025
Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Sin Ta Yi Rawar Gani A Fannin Bunkasa SCO

Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Sin Ta Yi Rawar Gani A Fannin Bunkasa SCO

August 25, 2025
CGTN Poll: Ba Da Kariya Shi Ne Tuna Baya—-Shekaru 80 Bayan Yakin Duniya Na II

CGTN Poll: Ba Da Kariya Shi Ne Tuna Baya—-Shekaru 80 Bayan Yakin Duniya Na II

August 25, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Hasashen Ambaliyar Ruwa A Jihohin Arewa 15

Gwamnatin Tarayya Ta Sake Gargadin Jihohin Arewa 9 Kan Afkuwar Ambaliya 

August 25, 2025
Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 3 Da Kubutar Da Mutum 16 Da Aka Sace A Kaduna

ECOWAS Za Ta Kaddamar Da Rundunar Yaki Da Ta’addanci Mai Jami’ai 260,000

August 25, 2025
Za A Watsa Shirin “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” a Manyan Kafofin Watsa Labarai Na Kasashen SCO

Za A Watsa Shirin “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” a Manyan Kafofin Watsa Labarai Na Kasashen SCO

August 25, 2025
Mauludi: Gwamnatin Kano Ta Sake Ɗage Ranar Komawa Makarantu

Zargin Babban Hadimin Gwamnan Kano Ya Karkatar Da Kuɗaɗen Jama’a Ba Gaskiya Ba Ne

August 25, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.