ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Fatara Da Talauci Na Yi Wa ‘Yan Nijeriya Miliyan 13 Barazanar Fadawa Kangin Talauci A 2025 — Rahoto

by Khalid Idris Doya and Sulaiman
2 years ago
Talauci

Hauhawar farashin kayayyakin masarufi, tashin kudin ruwa da kuma rugujewar darajar naira ka iya kwasan wasu karin ‘yan Nijeriya miliyan 13 ya jefa su cikin kangin talauci da fatara a shekarar 2025, a cewar rahoton ‘Pricewaterhouse Coopers (PwC) International Limited’.

Rahoton mai taken: Kasafin Nijeriya na 2025 da yanayin tattalin arzikinta, wanda PwP ta wallafa a shafinta: www.pwc.com ta lura da matsaloli da kalubalen tattalin arziki da Nijeriya ke fuskanta.

  • An Samu Ci Gaba A Bangaren Kayayyakin Da Sin Ta Fitar Zuwa Kasashe Da Yankuna 160 A 2024
  • Gwamnati Ta Sake Haɗa Tubabbun Mayaƙan Boko Haram 5,000 Da Iyalansu

Rahoton ya yi nuni da halin tattalin arzikin Nijeriya da dora shi a kan mizanin tashin farashin kayan masarufi da tsadar rayuwa da matsi da ake kara shiga na kan gaba wajen jefa jama’a cikin talauci, lamarin da ke dagula sha’anin ‘yan kasar musamman yanayin walwalarsu.

ADVERTISEMENT

Rahoton na PwC ya yi harsashen karuwar matalauta sosai a Nijeriya ne bisa dogara da rahoton kididdigar talauci na kasa da kasa (MPI) ta 2022.

Haka kuma rahoton ya shelanta cewa ‘yan Nijeriya miliyan 133 a halin yanzu wato kaso sama da 60 na yawan al’umman Nijeriya sun kasance matalauta ne sosai da suke da karancin samun ababen more rayuka kamar kiwon lafiya, ilimi, ayyukan yi, da kuma karancin yanayin rayuwa mai inganci.

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

A sabon rahoton 2024 da Bankin Duniya ya fitar, ya ce a kalla ‘yan Nijeriya miliyan 129 ne suke rayuwa cikin talauci, da ke nuni da cewa an samu kari fadawar mutane cikin talauci daga kaso 40.1 a 2018 zuwa kaso 56 a 2024.

Tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da ita tare da karuwar yawan jama’a cikin sauri, ya tsananta matakan talauci. Raguwar tattalin arziki kasar ga kowane mutum, wanda ya ragu da kashi 25.04 cikin dari daga dala 2,162.6 a 2022 zuwa dala 1,621.1 a 2023, ya kara jaddada raguwar karfin saye da kuma tabarbarewar rayuwa bisa ga rahoton PWC.

Tashin farashin kayayyaki shi ne ke kan gaba wajen janyo wa tattalin arzikin Nijeriya matsaloli. Zuwa watan Disamban 2024, kason hauhawar farashin kayan masarufi ya kai zuwa kaso 34.8 lamarin da ke kara lafta wa ‘yan Nijeriya damuwuwi musamman na yadda suke kasa iya sayen ababen bukata kama daga kayan abinci, gidaje da kuma kiwon lafiya.

Daga watan Janairu zuwa Satumban 2024, sufuri da kayan abinci su ne aka samu karuwa sosai a kansu. Tashin kudin man fetur shi ne ya janyo dukkanin tashin kudin sufuri da na kayan abinci.

Karuwar farashin kayan abinci na nuni da barazanar adana abinci da ake ciki, wanda ya shafi ‘yan Nijeriya miliyan 25.1 a 2024. Sai dai rahoton na PwP ya yi gargadin cewa adadin zai iya karuwa zuwa miliyan 33.1 a 2025 muddin hauhawar farashin ya ci gaba da tashi.

Duk da cewa gwamnatin tarayya ta biyo da wasu tsare-tsaren da take ganin za su saukaka kamar karancin albashi, sai dai kaso 4.1 cikin 100 kacal na ‘yan kasar ne ke aiki, lamarin da ke nuni da cewa hakan ba zai yi tasiri ba.

Masu ruwa da tsaki sun lura da cewa lamarin karuwar masu fadawa cikin talauci lamari ne da ke bukatar daukan matakan gaggawa na shawo kan matsalolin da suka dabaibaye tattalin arziki. Duk da karuwar tattalin arzikin Nijeriya na GDP da kaso 3.0 a 2024 akwai bukatar kara himma a 2025.

Rahoton ya yi kira da a samar da ingantattun matakan kawar da fatara, gami da sa kaimi ga al’umma da gyare-gyaren tsari don magance hauhawar farashin kayayyaki da bunkasar tattalin arziki mai dorewa.

A cewar rahoton, idan ba a dauki kwakkwaran mataki ba, matsalar tattalin arzikin da miliyoyin ‘yan Nijeriya ke fuskanta zai kara tabarbarewa tare da jefa dimbin iyalai cikin fatara da kuma kawo cikas ga ci gaban kasar na dogon lokaci.

Talauci
Khalid Idris Doya
+ posts Bio
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Yaro Ya Harbe Kansa Har Lahira Bayan Mafarauci Ya Yi Sakaci Da Bindigarsa A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    An Kama Mutane 5 Da Sassan Jikin Ɗan’Adam Za Su Yi Tsafi A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Tsohon Mai Neman Takarar Gwamnan Bauchi, Bala Jibrin, Ya Fice Daga APC Kan Zargin Ɗoki-ɗora
Talauci
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

MASU ALAKA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Next Post
gombe

Gwamnan Gombe Ya Jaddada Aniyarsa Ta Inganta Fannin Shari'a

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.