Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya shaida cewar gwamnatin tarayya ita kadai ba za ta iya daukan dawainiyar kudaden da sashin ilimi ke bukata a Nijeriya ba.
Ya shaida hakan ne a Abuja a yayin wani taro da aka shirya domin karrama Dakta Emeka Offor da matarsa, Dakta Adaora Offor wadanda suka samu lambar yabon digiri ta karramawa a bangaren tafiyar da harkokin kasuwanci da kuma shawarorin zamantakewa wanda jami’ar Nigeria Nsukka (UNN) da jami’ar Nnamdi Azikiwe (NAU), Awka suka ba su.
- Yadda Rashin Isassun Malaman Turanci Da Lissafi Ke Shafar Ingancin Ilimi A Nijeriya(2)
- Sabuwar Shekarar Musulunci: Fityanul Islam Ta Zaburar Da Musulmi Kan Bin Addini
Ministan ya ce gwamnati na kashe maguden kudade wajen daukan nauyin ilimi, don haka akwai bukatar daidaikun mutane da masu hannu da shuni da su kwaikwayi abun da Mista Offor da matarsa suka yi ta hanyar gidauniyarsu na taimakon ilimi.
Ya ce, “Ma’aikatarmu tana karfafan irin wannan karamcin, saboda gwamnati ba za ta iya dauke dawainiyar kudaden ilimi ita kadai ba, domin tana ba da gudunma-wa sosai.
“Wannan dalilin ne ya sanya mutane irin su Emeka Offor da matarsa suka shigo cikin lamarin, sannan akwai bukatar a karfafa musu guiwa. Na yi amanar wannan shi ne irin misalin kashe kudade ta hanyoyin da suka dace, don haka, ina kira ga sauran masu hannu da shuni da su yi koyi da abun da su din suka yi.”
Yayin da jami’ar UNN ta amshi naira miliyan 100 domin harkokin da suka shafi zurfafa bincike da nazarin ilimi tare da masana harkokin kasuwanci domin ingant-awa da tabbatar da yin tasiri a tsangayar koyar da ilimin harkokin gudanar da kasuwanci, inda ita kuma jami’ar NAU ta amshi naira miliyan 50 a matsayin tal-lafin kula da walwalar zawarawa, yara da suke fama da bukata ta musamman da kuma sauran jama’a da ke cikin yanayi na fatara.
Mai ba da tallafin, Cif Offor ya ce, wannan tallafin ba shi ne na karshe ba, kuma za su ci gaba da yin duk mai yiyuwa domin taimaka wa jami’o’in Nijeriya.
Ya ce, “Wannan tallafin na daga cikin manufarmu na ganin mun taimaka wa ilimi a manyan matakai a Nijeriya,” sai ya nemi karin hadin guiwa a tsakanin gidauniyar-sa ta SEOF da kuma jami’o’in UNN da NAU.