Tallafin man fetur da gwamnati mai ci ke biya yanzun, ya ninka abinda ake biya a baya ba tare da sanin ‘yan Nijeriya ba.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin da yake zantawa da manema labarai a Maiduguri babban birnin jihar Borno.
- Farashin Kayan Masarufi Ya Sake Tashi Zuwa Kashi 33.2 A Nijeriya – NBS
- Mene Ne Dalilin Da Ya Sa Japan Ke Daukar Wasu Matakan Da Ka Iya Haifar Da Hadari?
El-Rufai ya ce, duk da ya goyi bayan tsarin cire tallafin, amma ya soki yadda aka aiwatar da shi.
Ya kara da cewa, matakan da Gwamnatin Tarayya ta dauka na bayar da kunshin kyauta a matsayin tallafin rage radadin cire tallafin man fetur ba su yi tasiri ba, don haka aka koma ga tsarin tallafin biyan tallafin.