Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin ƙara farashin wutar lantarki a watanni masu zuwa, tana mai cewa hakan ya zama dole domin samar da tsarin farashin da ya dace da kuɗin aiki, wanda zai jawo zuba hannun jari daga fannoni masu zaman kansu a ɓangaren makamashi.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin makamashi, Olu Verheijen, ne ya bayyana hakan a taron shugabannin ƙasashen Afrika kan makamashi da aka gudanar a Dar es Salaam, Tanzaniya, inda Nijeriya ta gabatar da shirin dala biliyan 32 na faɗaɗa samar da wuta zuwa shekarar 2030.
- An Sace Kayayyakin Turakun Wutar Lantarki 18 A Cikin Kwanaki 6 – TCN
- Jami’in Kenya: Fasahar Sin Na Ingiza Samar Da Wutar Lantarkin Kenya
Ta ce duk da cewa za a daidaita farashin wutar domin ya yi dai-dai da kuɗin aiki, gwamnati na da niyyar kare masu ƙaramin ƙarfi ta hanyar bayar da tallafi. Wannan shirin na ƙarin farashin ya biyo bayan matakin da gwamnati ta ɗauka a bara na ƙara farashin wuta har sau uku 300% ga masu amfani da rukunin A.